"Ka Kore Su": Jigon APC Ya Ba Shugaba Tinubu Lakanin Gyara Najeriya

"Ka Kore Su": Jigon APC Ya Ba Shugaba Tinubu Lakanin Gyara Najeriya

  • Wani jigo a jam'iyyar APC mai mulki ya fito ya gayawa shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya kamata ya bi domin gyara ƙasar nan
  • Jesutega Onokpasa ya buƙaci Tinubu da ya kori tawagar ƴan Legas da ke tattare da shi tare da maye gurbinta da tawagar ƴan Najeriya
  • Ɗan a mutun na Shugaba Tiinubu ya bayyana cewa kuskure ne tunanin cewa tawagar ƴan Legas za ta taimaka masa a gyara Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Wani jigo a jam’iyyar APC, Jesutega Onokpasa, ya ba shugaban ƙasa Bola Tinubu, shawara kan hanyar gyara Najeriya.

Jesutega ya shawarci Tinubu da ya samar da ƙwararrun ƴan Najeriya a kusa da shi domin ya samu damar gyara kura-kuran da gwamnatocin baya suka yi da kuma cimma tsare-tsarensa kan tattalin arziƙin Najeriya.

Kara karanta wannan

Atiku ya caccaki Tinubu, ya bayyana inda gwamnatinsa ta samu matsala

Jigon APC ya ba Tinubu shawara
Jigon APC ya bukaci ya samar da tawagar kwararrun 'yan Najeriya a kusa da shi Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Wace shawara jigon APC ya ba Tinubu

Jesutega Onokpasa, wanda ɗan a mutun Tinubu ne, ya buƙace shi da ya tarwatsa tawagar ƴan Legas da ke kewaye da shi, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jigon na APC ya buƙaci Shugaba Tinubu ya haɗa tawagar ƴan Najeriya da za su taimaka masa wajen cimma burinsa na dawo da ƙasar nan kan turba, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.

Jesutega wanda 'dan kwamitin yakin neman zaɓen shugaban ƙasan Bola Tinubu a 2023 ne, ya ce ƴan Legas da ke tattare da shi ba su taɓuka komai kuma ba su da wata ƙima a gwamnatinsa.

"Shugaban ƙasa, yawancin mu mun goyi bayanka ne saboda mun san abin da ka yi a Legas."
"Amma ba za ka haɗa wata tawaga wacce gaba ɗayanta ƴan Legas ne ba ka ce za ka gyara Najeriya, wannan kuskure ne. Za ka iya haɗa tawagar ƴan Legas domin su gyara Legas, amma kana buƙatar haɗa tawagar ƴan Najeriya domin gyara Najeriya."

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Babban jigo ya faɗi dalili 1 da ya kamata a tsige Tinubu da wasu gwamnoni

"Waɗannan ƴan Legas ɗin da ka kawo Abuja domin taimaka maka gyara Najeriya, ba su taimakonka. Ya kamata ka kore su. Cikin girmamawa shugaban ƙasa kana buƙatar ka kori wannan tawagar ka haɗa wacce ta ƙunshi ƴan Najeriya."
"Dole ne ya kasance na kusa da kai ba tawagar ƴan Legas ba ce, dole ne ta kasance tawagar ƴan Najeriya. Idan ba haka babu wani sauyi da za a samu. Da yawa daga cikinsu kuɗi kawai suka sa a gaba ba ƙaunar nasarar ka suke yi ba."

- Jesutega Onokpasa

Karanta wasu labaran kan Tinubu

Atiku ya caccaki Shugaba Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya sake caccakar gwamnatin APC ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Olusegun Obasanjo ya fadi hanyar da Najeriya za ta samu ci gaba

Atiku ya ce idan har yanzu APC ba ta gane irin wahalhalun da ƴan Najeriya ke ciki ba, hakan na nufin tun farko ba ta shirya yin mulkin ƙasar nan ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng