Tinubu ya Kawo Wata Doka a Harkar Lafiya, Likitoci Za su Daina Tafiya Ketare

Tinubu ya Kawo Wata Doka a Harkar Lafiya, Likitoci Za su Daina Tafiya Ketare

  • Shugaban kasa Bola Tinubu ya kawo dakar da za ta canza tsarin da ya ba likitocin Najeriya fita zuwa kasashen waje sakaka
  • Gwamnatin tarayya ta ce an kawo dokar ne domin inganta lafiyar yan kasa wajen samar da wadatattun ma'aikatan lafiya a Najeriya
  • Ministan lafiya na kasa, Farfesa Muhammad Ali Pate ya fadi tanadin da suka yi wa likitocin da za su cigaba da aiki a gida

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da dokar da za ta hana likitocin Najeriya tafiya ketare.

A jiya Litinin ne gwamnatin tarayya ta sanar da haka tare da faɗin shirye shiryen da suka yi a kan sabuwar dokar.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe Kyaftin Ibrahim, Jarumin sojan Najeriya ya rasa rayuwarsa

Bola Tinubu
Tinubu ya kawo dokar da ta shafi likitoci. Hoto: @muhammadpate
Asali: Twitter

Legit ta tattaro abin da dokar ta kunsa ne a cikin wani sako da ministan lafiya na kasa, Farfesa Muhammad Ali Pate ya wallafa a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dokar hana likitocin Najeriya fita waje

Shugaban kasa Bola Tinubu ya sanya hannu kan dokar hana likitocin Najeriya fita aiki kasashen ketare.

Ministan lafiya, Farfesa Muhammad Pate ya ce wannan na cikin kokarin gwamnatin tarayya wajen inganta lafiya a Najeriya.

Inganta ma'aikatun lafiya a Najeriya

Ministan lafiya ya ce yawanci likitoci na tafiya kasar waje ne saboda yanayin aiki marar ɗaɗi' amma ya ce an dauko matakin gyara.

Farfesa Pate ya ce za a kawo tsare tsare sababbi da za su inganta lafiyar likitoci da walwalarsu a Najeriya.

Maganar dawo da likitocin daga ƙetare

Haka zalika ministan lafiya ya ce bayan hana likitoci fita waje za a fara dawo da likitocin Najeriya da suke aiki a kasashen ketare.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da bankadar Dan Bello, Tinubu ya dakatar da aikin hanyar Kano zuwa Maiduguri

Farfesa Pate ya ce za a bude yadda likitocin Najeriya da suke waje za su yi rajista domin dawowa gida kuma za a samar da hanyoyin karfafa musu gwiwa.

Tinubu ya shirya taro majalisar magabata

A wani rahoton, kun ji cewa a yau Talata ne mai girma Bola Ahmed Tinubu ya shirya taron majalisar magabata na kasa a fadar shugaban kasa.

Rahotanni sun nuna cewa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa fadar a karon farko tun saukarsa a mulkin Nijeriya a shekarar 2023.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng