Ambaliya: Ruwa Kamar da Bakin Kwarya Ya Jawo Gidaje Sama da 100 Sun Ruguje a Jigawa

Ambaliya: Ruwa Kamar da Bakin Kwarya Ya Jawo Gidaje Sama da 100 Sun Ruguje a Jigawa

  • Mazauna garin Gantsa da ke karamar hukumar Buji a jihar Jigawa sun fada mawuyacin hali sakamakon mamakon ruwa
  • Ruwan saman da ya rika zuba kamar da bakin kwarya ya lalata gidaje sama da 100 yayin da jama'a su ka fara gudun neman tsira
  • Jami'in hulda da jama'a na hukumar tsaron fararen hula (NSCDC), Badrudeen Tijjani Mahmud ya tabbatarwa Legit aukuwar mummunar ambaliyar

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Jigawa - Mazauna garin Gantsa a karamar hukumar Buji da ke Jigawa sun fara gudun tsira bayan mamakon ruwa da ya sauka a yankin. Zuwa yanzu an tabbatar da rushewar gidajen jama'a sama da 100, yayin da ruwan ya mamaye garin saboda rashin hanyar da ruwan zai wuce.

Kara karanta wannan

"Ko mutum 1 ba a kashe a lokacin zanga zanga ba," Inji rundunar 'yan sandan Kano

Jigawa
Ruwan sama ya lalata muhallai a Jigawa Hoto: Badruddeen Tijjani Mahmud
Asali: Facebook

Jami'in hulda da jama'a na rundunar tsaron farin kaya (NSCDC), Badrudeen Tijjani Mahmud ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa lamarin ya afku a ranar Litinin din nan.

Ambaliyar ruwa ta rusa gidajen mutane

Duk da mamakon ruwan da aka tafka a karamar hukumar Buji a Jigawa bai jawo asarar rayuka ba, amma ya raba jama'a da matsugunansu, inda ake barin garin domin neman mafaka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin rundunar NSCDC a jihar, Badrudeen Tijjani Mahmud ya tabbatarwa Legit cewa jami'ansu na kokarin kare dukiyar jama'ar garin Gantsa daga miyagun da ka iya sace su.

Ya ce har yanzu ana aikin ceto domin tallafawa wadanda gidajensu su ka ruguje, yayin da hukumar bayar da agaji a matakin farko (NEMA) ke kiyasta asarar da aka tafka.

Mutane sun makale bayan ambaliya a Abuja

Kara karanta wannan

Direban adaidaita sahu ya maida jakar kudin da ya tsinta, yan sanda sun sa cigiya

A baya kun samu labarin cewa mamakon ruwan sama ya sa mutane da dama sun shiga mawuyacin hali bayan gidajensu da ababen hawa sun nutse a cikin ruwan da aka dade ana yi.

An gano yadda mazauna Trade Moore Estate a Abuja su ka yi cirko-cirko yayin da wasu su ka dukufa domin aikin ceton wadanda su ka malake a cikin ruwan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.