Cikakken Jerin Matatun Mai Guda 10 Mafi Girma a Duniya

Cikakken Jerin Matatun Mai Guda 10 Mafi Girma a Duniya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Matatun mai da ke aikin sarrafa ɗanyen man fetur zuwa abubuwa da dama na da matuƙar muhimmanci ga tattalin arziƙin duniya.

Suna da matuƙar girma wanda hakan ya sanya samar da su ya ke buƙatar zuba hannun jari mai yawan gaske.

Matatun mai mafi girma a duniya
Matatar mai ta Dangote na daga cikin matatun mai mafi girma a duniya Hoto: Bloomberg
Asali: UGC

Yawan matatun mai a duniya

A halin yanzu akwai matatun mai guda 825 da ke aiki a duniya, cewar rahoton jaridar Businessday.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga cikin waɗannan matatun mai, ƙasar Amurka ce ke da mafi yawa daga ciki, daga nan sai ƙasar China da Rasha.

Matatar man Dangote da ke Najeriya na ɗaya daga cikin manyan matatun mai a duniya.

Kara karanta wannan

Sanata daga Arewa ya yi nasara a kotun ɗaukaka ƙara, ya tabbata cikakken ɗan APC

Matatun mai mafi girma a duniya

Jaridar The Nation ta tattaro matatun mai mafi girma guda 10 a duniya. Ga jerinsu nan ƙasa:

1. Matatar mai ta Jamnagar, India

Matatar mai ta Jamnagar da ke a jihar Gujarat ta ƙasar India, ita ce mafi girma a duniya.

Matatar wacce take mallakin kamfanin Reliance, tana tace ɗanyen mai ganga 1.24m a kowace rana.

2. Matatar mai ta Paraguana, Venezuela

Matatar mai ta Paraguana mallakin kamfanin man fetur na ƙasar Venezuela, (PDVSA) ce.

Matatar wacce ita ce ta biyu mafi girma a duniya tana a yankin Paraguana na ƙasar Venezuela. Tana tace ganga 940,000 a kowace rana.

3. Matatar mai ta Ulsan, South Korea

Matatar mai ta Ulsan wacce mallakin kamfanin SK Energy ce na ƙasar South Korea, ita ce ta uku mafi girma a duniya.

Matatar wacce take a yankin Ulsan, tana tace ganga 900,000 a kowace rana.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Babban jigo ya faɗi dalili 1 da ya kamata a tsige Tinubu da wasu gwamnoni

4. Matatar mai ta Ruwais, UAE

Matatar mai ta Ruwais mallar kamfanin man fetur na haɗaɗɗiyar daular Larabawa, (ADNOC) ce.

Matatar wacce take a Ruwais na ƙasar UAE, tana tace ganga 827,000 a kowace rana.

5. Matatar mai ta Yeosu, South Korea

Matatar mai ta Yeosu mallakin kamfanin GS Caltex ce na ƙasar South Korea. Matatar tana samar da ganga 840,000 a kowace rana.

6. Matatar mai ta Onsan, South Korea

Matatar mai ta Onsan a ƙasar South Korea, mallakin kamfanin S-Oil Corporation ce.

Matatar wacce ita ce ta shida mafi girma a duniya, tana samar da ganga 669,000 a kowace rana.

7. Matatar mai ta Dangote, Najeriya

Matatar mai ta Dangote tana a Lekki da ke jihar Legas a Najeriya. Matatar wacce mallakin kamfanin Dangote ce, ita ce ta bakwai mafi girma a duniya.

Matatar mai ta Dangote za ta iya samar da ganga 650,000 a kowace rana.

Kara karanta wannan

Cikakken jerin kasashen Afirika 10 masu yawan arzikin man fetur

8. Matatar mai Galveston Bay, Amurka

Matatar mai ta Galveston Bay mallakin kamfanin Marathon Petroleum Corporation ne da ke ƙasar Amurka

Matatar wacce take a jihar Texas tana samar da ganga 631,000 a kowace rana.

9. Matatar mai ta Beaumont, Amurka

Matatar mai ta Beaumont da ke a ƙasar Amurja mallakin kamfanin ExxonMobil ce.

Matatar wacce take a yankin Beaumont na jihar Texas, tana samar da ganga 630,000 a kowace rana.

10. Matatar mai ta Port Arthur, Amurka

Matatar mai ta Port Arthur wacce mallakin kamfanin Motiva Enterprises ce, ita ce ta 10 mafi girma a duniya.

Matatar wacce take a jihar Texas ta ƙasar Amurka, tana samar da ganga 600,000 a kowace rana.

Dangote zai siyar da wani kaso a matatar mansa

A wani labarin kuma, kun ji cewa ce Aliko Dangote na shirin sayar da kashi 12.75 na hannun jarin matatar man Dangote saboda matsalar kuɗi.

An ce Dangote na shirin yin amfani da kuɗin da ya samu daga hannun jarin da zai sayar domin biyan wani bashi mai yawa wanda wa'adinsa zai cika a ranar 31 ga Agusta, 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng