Gwamna Ya Janye Dokar Hana Fita a Kaduna da Zaria, Ya Aikawa Malamai, Sarakuna Saƙo
- Malam Uba Sani ya janye dokar hana fita gaba ɗaya a cikin garin Kaduna da Zaria bayan abubuwan da suka afku lokacin zanga zanga
- Kwamishinan tsaron cikin gida ya ce daga yanzu jama'a na da damar gudanar da harkokinsu na halak ba tare da wata tsangwama ba
- Gwamna ya godewa hukumomin tsaro, malamai, sarakuna da sauran masu ruwa da tsaki bisa rawar da suka taka wajen magance lamarin
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna - Gwamna Uba Sani na Kaduna ya cire dokar hana fita daga karfe 6 na yamma zuwa karfe 8 na safe da ya sanya sakamakon tashe-tashen hankulan da suka faru lokacin zanga-zanga.
Gwamnan Uba Sani ya ce janye dokar zai fara aiki ne daga ranar Talata, 13 ga watan Agusta kuma mutane na da damar ci gaba da harkokinsu na yau da kullum.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a safiyar yau Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Kaduna ta janye dokar kulle
Ya bayyana cewa hakan na nufin jama'a na da ‘yancin ci gaba da gudanar da halastattun harkokunsu na yau da kullum a Kaduna da Zariya ba tare da takura ba.
Aruwan ya ce a zaman majalisar tsaron Kaduna karƙashin jagorancin Malam Uba Sani, an yi nazari mai zurfi tare da amincewa da janye dokar kullen gaba ɗaya.
A cewarsa, majalisar tsaron ta ja kunne da kashedi kan duk wani taro ko gangami da za a yi a faɗin kaduna ya zama dole a nemi sahalewar hukumomin tsaro.
Uba Sani ya godewa malamai da sarakuna
Samuel Aruwan ya ce jami'an tsaro za su ci gaba da sa ido domin daƙile duk wata barazanar tarwatsa zaman lafiya tare da ɗaukar mataki kan duk mai kunnen ƙashi.
Kwamishinan ya ce:
"Gwamna Sani wanda ya jagoranci taron, ya yabawa shugabannin tsaro, malamai, sarakuna a, da duk masu ruwa da tsaki bisa rawar da suka taka wajen dakile abubuwan da suka faru a Kaduna da Zariya."
Ibrahim Bala, wani tela kuma mai sayar da yadi a kasuwar Barci da ke cikin garin Kaduna ya ce sun ji daɗin cire dokar amma ba ƙaramin takura masu a ka yi ba da farko.
Magidancin ya shaidawa Legit Hausa cewa mutane da dama sun takura, sun shiga wahala saboda sai sun fita suke samun abin da za su ba iyalansu.
Ibrahim ya ce:
"Ƴan kwanakin nan da aka kulle mu mun sha wahala dama kuma ga halin da ake ciki, gwamnati fa ta san duk masu aikata laifin to mu ina ruwan mu?"
Gwamnan Filato ya rage dokar zaman gida
Kun ji cewa Gwamna Caleb Mutfwang na Filato ya ƙara sassauta dokar hana zirga-zirga a Jos, babban birnin jihar daga ranar Talata
Daga yanzun mazauna Jos na da ikon fitowa su yi harkokinsu na yau da kullum daga karfe 7:00 na safe zuwa 7:00 na yammaci.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng