'Yan China Sun Faɗa Tarkon Ƴan Bindiga a Najeriya, Sun Turo Saƙo Mai Ɗaga Hankali

'Yan China Sun Faɗa Tarkon Ƴan Bindiga a Najeriya, Sun Turo Saƙo Mai Ɗaga Hankali

  • Ƴan bindiga sun yi garkuwa da ƴan ƙasar China biyu da suka shigo Najeriya domin yin aiki a jihar Ogun
  • Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, Omolola Odutola ta ce jami'an haɗin guiwa na neman ceto su
  • Ta ce sun samu labari maharan sun kira waya, sun fara neman a biya kuɗin fansa kafin su sake mutanen nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ogun - Ƴan bindiga sun yi garkuwa da wasu ‘yan kasar China biyu a yankin kauyen Kemta da ke kan titin Onigbedu a karamar hukumar Ewekoro ta jihar Ogun.

Jami'ar hulɗa da jama'a ta rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, Omolola Odutola, ta tabbatar da faruwar lamarin ranar Litinin a Abeokuta.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun gano babban wanda ake zargi da tsara 'rusa' Najeriya lokacin zanga zanga

Taswirar jihar Ogun.
Yan bindiga sun yi garkuwa da ƴan China, sun nemi kuɗin fansa a Ogun Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Kamar yadda Channels tv ta ruwaito, Odutola ta bayyana cewa dakarun ƴan sanda sun bazama da nufin ceto waɗanda maharan suka sace.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masu garkuwa da 'yan China sun turo saƙo

Jami'ar ta kuma ƙara cewa rundunar ƴan sanda ta samu labarin masu garkuwa da mutanen sun tuntubi kamfaninsu da ƴan Chinan ke aiki domin neman kudin fansa.

Mai magana da yawun ƴan sandan ta ce jami'an tsaron haɗin guiwa sun shiga dajin da ke yankin sun bincika ko'ina amma ba su ga waɗanda aka sace ba.

Jami'an tsaro sun shiga daji

"Mai kula da harkokin tsaro na kamfanin ya ce daya daga cikin 'yan kasar wajen ya kira shi ya sanar da shi cewa an yi garkuwa da Wenguang da Ding kuma masu garkuwan suna neman kudi domin a sako su."
"Ƴan sanda na caji ofis sin Ewekoro tare da ’yan banga, sojoji, mafarauta da sauran kungiyoyin tsaro, sun bincike dajin Kémta baki daya domin ceto wadanda aka sace amma ba su gansu ba.”

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun canza salon ta'addanci, sun budewa motar fasinjoji wuta

- Omolola Odutola.

Kakakin ƴan sandan ta ce duk da haka dakaru na ci gaba ɗaukar matakai da bincike domin tabbatar da an kubutar da ƴan Chinan da aka sace cikin ƙoshin lafiya, Tribune Nigeria ta rahoto.

Yan bindiga sun kai harin bom

A wani rahoton kun ji cewa ƴan bindiga sun kai mummunan hari kan ƴan sanda a shingen binciken ababen hawa a jihar Anambra da ke Kudu maso Gabas.

Rundunar ƴan sanda ta ce maharan sun yi amfani da bom suka kashe ɗan sanda ɗaya a harin tare da jikkata wani mutum ɗaya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262