Yan Kasuwa Sun Yi Hasashen Saukar Farashin Litar Man Fetur daga kusan N1000
- Yan kasuwa sun yi hasashen samun sauƙin farashin man fetur yayin da ake tsammanin fara samun tataccen mai daga matatar Dangote
- Mataimakin shugaban kungiyar yan kasuwar man fetur ta kasa (IPMAN), Hammed Fashola ne ya bayyana haka ga manema labarai
- Hammed Fashola ya fadi babban dalilin da yasa kungiyar IPMAN ke tsammanin samun sauƙin farashin man fetur daga matatar Dangote
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Kungiyar yan kasuwar man fetur ta kasa (IPMAN) ta yi hasashen samun sauki kan farashin man fetur.
IPMAN ta yi hasashen ne yayin da matatar Dangote da ke jihar Legas ke shirin fara fitar da da tataccen mai.
Jaridar Punch ta wallafa cewa mataimakin shugaban kungiyar IPMAN, Hammed Fashola ne ya yi hasashen.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin samun sauƙin man fetur
Mataimakin shugaban kungiyar IPMAN, Hammed Fashola ya ce akwai yiwuwar samun sauƙin man fetur nan gaba kadan.
Hammed Fashola ya ce akwai tsammanin farashin zai karye da zarar matatar Dangote ta fara fitar da man fetur a wannan watan.
Fashola ya fadi haka ne kasancewar farashin man dizil ya karye daga N1,600 zuwa N1,150 a lokacin da matatar Dangote ta fara fitar da shi kasuwa.
Ya farashin fetur yake a Najeriya?
Daily Post ta wallafa cewa Hammed Fashola ya bayyana cewa suna sayen man fetur ne a N700 ya yi sama duk lita a wajen yan kasuwa.
Amma ya ce akwai tsammanin samun sauƙin farashin zuwa N600 da zarar matatar Dangote ta fara fitar da mai zuwa kasuwa.
Sai dai Hammed Fashola ya ce samun sauƙin ya dangana ne da kudin da matatar ta kashe wajen aikin tace danyen mai.
Legit Hausa ta fahimci cewa a wasu garuruwan Arewa, bayan zanga-zangar da aka yi an koma saida lita tsakanin N850-N950.
Matatar Dangote: Atiku ya yi magana
A wani rahoton, kun ji cewa Atiku Abubakar, ya yi gargaɗi kan duk wani yunƙuri da ake yi na kawo cikas ga ci gaban matatar man Dangote.
Atiku Abubakar ya kuma yi kira ga ƴan Najeriya da gwamnati mai ci da su bayar da cikakken goyon baya ga matatar man Dangote.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng