El Rufai Ya Sake Burmawa Matsala da Ake Zargin Mutuminsa Kan Zambar N11bn

El Rufai Ya Sake Burmawa Matsala da Ake Zargin Mutuminsa Kan Zambar N11bn

  • Hukumar yaki da cin hanci ta ICPC ta bukaci sanya ido kan tsohon hadimin Nasir El-Rufai kan badakalar kudi
  • Ana zargin Mr. Jimi Lawal da badakalar N11bn kan aikin kwangilar jirgin kasa maras daukar kaya ba bisa ka'ida ba
  • Hukumar ta gayyaci Lawal ya gurfana a gabanta a jiya Litinin 12 ga watan Agustan 2024 amma ya ki halarta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon hadimin Mallam Nasir El-Rufai ya shiga tarkon hukumar yaki da cin hanci ta ICPC.

Wanda ake zargin, Mr. Jimi Lawal ya samu gayyatar hukumar ICPC domin amsa tambayoyi kan zargin badakalar N11bn.

Kara karanta wannan

Ana rade radin gwamnan PDP zai sauya jam'iyya, tsageru sun jefa 'bam' ofishin APP

Hukumar ICPC na tuhumar tsohon hadimin Nasir El-rufai
Hukumar yaki da cin hanci ta ICPC ta baza komarta kan tsohon hadimin Nasir El-rufai. Hoto: Nasir El Rufai.
Asali: Facebook

ICPC na neman hadimin El-Rufai kan badakala

Hukumar ta gayyaci Lawal ne saboda zargin almundahana a kwangilar jirgin kasan cikin gari, The Nation ta tattaro labarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana zargin babu wani yarjejeniya na kwangila kan aikin da aka gudanar amma an biya kudin gaba daya.

An gayyaci Lawal ne a jiya Litinin 12 ga watan Agustan 2024 amma ya ki halartar zaman kuma bai tura wani wani wakili ba, cewar Pulse.

ICPC ta bukaci taimakon DSS & NIS

ICPC ta bukaci hukumar DSS da hukumar shige da fice ta NIS domin sanya ido kan wanda ake zargi a filayen jirgin sama da sauran iyakoki.

Har ila yau, hukumar ta na zargin Lawal da karbar basuka na gida da ketare ba tare da bin ka'idoji ba.

Wata majiya daga hukumar ICPC ta ce ta samu korafe-korafe kan gwamnatin Nasir El-Rufa'i da ta shude.

Kara karanta wannan

Taraba: Kungiyar CAN ta ba da umarnin yin addu'o'i da azumi na kwanaki 3

Majiyar ta ce ICPC ta yi duba zuwa ga korafe-korafen inda ta ce ya zama dole ta yi kwakkwaran bincike mai zurfi kan abin da suka samu.

El-Rufai ya maka dan Majalisa a kotu

A wani labarin, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya maka 'dan Majalisar jihar, Henry Marah a kotu.

Nasir El-Rufai ya kuma yi karar wata tashar talabijin domin neman hakkinsa kan zargin badakalar N423bn.

Tsohon gwamnan ta bakin lauyansa, A U Mustapha ya ce hirar da aka gudanar ya saba doka wanda aka bata masa suna ba tare da hujja ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.