Gwamna Ya Haramtawa Hadimansa Fita daga Jiharsa, Ya Gindaya Kowa Sharadi

Gwamna Ya Haramtawa Hadimansa Fita daga Jiharsa, Ya Gindaya Kowa Sharadi

  • Gwamnatin jihar Adamawa ta dauki wani muhimmin mataki domin dakile yawan kashe kudi saboda tattalin arziki
  • Gwamna Ahmadu Fintiri ya dauki matakin hana hadimansa na siyasa fita wajen jihar idan gwamnati ce za ta dauki nauyi
  • Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da sakataren yada labaransa, Humawashi Wounosikou ya bayyanawa yan jaridu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Adamawa - Gwamna Ahmadu Fintiri na Adamawa ya haramtawa hadimansa fita wajen jihar game da sha'anin gwamnati.

Gwamnan ya dauki wannan mataki ne saboda rage yawan kashe-kashen kudi da ake yi a gwamnati duba da halin matsin tattalin arziki.

Gwamna Fintiri ya dakile hadimansa daga fita wajen jiharsa
Gwamna Ahmadu Fintiri ya hana hadimansa fita wajen jihar saboda tattalin arziki. Hoto: Ahmadu Umaru Fintiri.
Asali: Twitter

Tattalin arziki: Gwamna Fintiri ya dauki mataki

Kara karanta wannan

Rigima ta barke, mataimakin gwamna da majalisa ta tsige ya koma bakin aiki a ofis

Sakataren yada labaran gwamnan, Humawashi Wounosikou shi ya bayyana haka ga jaridar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wounosikou ya ce an dauki matakin ne tun bayan cire tallafin mai domin rage nauyin da ke kan jihar.

Sai dai ya ce idan har mutum zai fita wajen jihar to dawainiyar tafiyar tasa ba ta kan gwamnatin Adamawa

Matakin da Gwamna ya dauka kan hadimansa

"Mai girma gwamna ya duba halin da tattalin arziki ke ciki bayan cire tallafin mai, ya dauki mataki domin rage yawan kashe kudin jihar."
"Duka wadannan ayyuka da ke gudana a jihar ba za su samu ba idan ba tare da tsarin Fintiri wurin kula da tattalin arzikin ba."
"Saboda rage yawan kashe kudin, yana fita wajen jihar kan abin da ya shafi gwamnati ba tare da hadimansa ba."

- Humawashi Wounosikou

Wounosikou ya ce Fintiri na daga cikin gwamnonin Najeriya da suke da mafi karancin hadimai da mukarraban gwamnati saboda matsin tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Sakataren gwamnati ya yi murabus, gwamna ya naɗa wanda zai maye gurbin nan take

An dakawa motar taki wawa a Adamawa

A wani labarin, kun ji cewa wasu matasa sun farmaki babbar mota dauke da takin zamani inda suka afka mata gaba daya.

Babbar motar na makare da takin zamanin ne a kan hanyarta ta zuwa karamar hukumar Demsa da ke jihar Adamawa.

Rahotanni sun tabbatar da cewa takin na gwamnatin jihar ne domin rarrabawa manona a kokarin bunkasa harkokin noma.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.