Bayan Bidiyon Dan Bello, an Bankado Wata Badakalar N50bn a Jihar Kano
- Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a jihar Kano ta yi bayani kan badakalar kudi da ta binciko na sama da Naira biliyan 50
- Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa a jihar Kano, Muhyi Magaji Rimin Gado ne ya bayyana haka ga manema labarai
- Muhyi Magaji Rimin Gado ya bayyana babban kalubale da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ke fuskanta a jihar Kano
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Kano ta bankado yadda aka karkatar da kudi sama da N50bn a jihar.
Hakan na zuwa ne bayan tsohon kwamishinan ayyukan jihar ya gaskata labarin rashawa da mai bidiyon barkwanci, Dan Bello ya bankado.
Jaridar Aminiya ta wallafa cewa bayan N50bn din, hukumar ta gano wasu kudi da aka karkatar domin sayen gidan sauro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Maganar karkatar da N50bn a Kano
Shugaban hukumar yaki da rashawa ta jihar Kano, Muhyi Magaji Rimin Gado ya bayyana cewa yana da shaidu kimanin 145 kan zargin sace kudi N50bn a jihar da aka yi.
Muhyi Magaji Rimin Gado ya kara da cewa sun gano gidaje da otel da suke da alaka da kudin da aka sace daga asusun gwamantin jihar a Abuja, London da Dubai.
Ana zargin karkatar da N450m a Kano
Haka zalika hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta bayyana cewa tana zargin sace kuɗi N459m daga asusun jihar.
Daily Trust ta wallafa cewa Muhyi Magaji ya bayyana cewa suna zargin an sace kudin ne daka ware domin sayen gidan sauro.
Kano: Kalubalen hukumar yaki da rashawa
Hukumar yaki da rashawa ta ce ta yi yunkurin kama wanda ake zargi da karakatar da kudin sayen gidan sauro amma ya tafi kotu domin neman kariya wanda hakan ya kawo mata tasgaro.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gargadi jami'an gwamnati kan cewa ba zai yarda da satar kuɗin gwamnati a karkashin mulkinsa ba kwata kwata.
Rashawa: Abba ya yi magana kan Ganduje
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Kano ta bayyana damuwa kan yadda aka samu cin hanci fiye da ko yaushe a lokacin mulkin Abdullahi Ganduje.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce |Dr. Ganduje ya kassara jihar musamman wurin cin hanci da rashawa wanda ya yi muni sosai.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng