"Ko Mutum 1 ba a Kashe Lokacin Zanga Zanga ba," Inji Rundunar 'Yan Sandan Kano
- An samu rahotanni daga jama'a da hotunan da ke yawo a kafafen sada zumunta na mutuwar wasu mutanen Kano lokacin zanga-zanga
- Amma a yau Litinin, rundunar 'yan sandan Kano ta ce babu ko mutum guda da ya rasu ko aka harba a yayin nuna adawa da manufofin gwamnati
- Wannan ya zama amsa kuwwar Sufeta Janar na 'yan sanda da ya musanta cewa babu jami'in tsaron da ya yi harbi yayin zanga zangar
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Rundunar 'yan sandan Kano ta hakikance kan cewar babu mutumin da harbin bindiga ya yi sanadiyyar rasuwarsa yayin zanga zanga.
Kwamishinan 'yan sandan jihar, Salman-Dogo Garba ne ya bayyana haka ga manema labarai a zantawarsa da su a ofishin 'yan sandan Kano.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa kalaman kwamishinan na zuwa duk da an samu jama'ar da su ka tabbatar da rasuwar yan uwansu saboda harbin bindiga a lokacin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ba mu da rahoton mutuwar kowa' - Yan sanda
Rundunar 'yan sandan Kano ta tara manema labarai inda ta musanta cewa akwai jami'inta da ya harbi masu zanga zanga a makon da ya gabata a jihar, aminiya ta ruwaito wannan.
Kwamishinan yan sandan Kano, CP Salman Dogo da ya bayyana haka ya ce a dukkanin rahoton da su ka samu, babu inda aka ce an kashe wani ko wata.
'Yan kasar nan sun yi fitar dango domin zanga-zangar adawa da yadda gwamnati ta barsu cikin talauci da matsin rayuwa, inda daga bisani lamarin ya koma tashin hankali.
Sojoji sun tabbatar da harbin masu zanga-zanga
A baya mun ruwaito cewa rundunar sojoji ta kasa ta tabbatar harbin wasu daga cikin masu zanga-zanga har ta jawo asarar ran wani matashi a Samaru da ke Zaria, jihar Kaduna.
Wannan tabbaci na zuwa bayan rundunar 'yan sandan kasar nan, ta bakin babban Sufeto, Kayode Egbetokun ta karyata cewa an samu harbe-harben masu zanga zanga a kasar nan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng