"Babu Ruwan Tinubu," Dan majalisar APC Ya Yi Martani ga Gwamnan PDP kan Yunwa a Najeriya

"Babu Ruwan Tinubu," Dan majalisar APC Ya Yi Martani ga Gwamnan PDP kan Yunwa a Najeriya

  • Sanata Shehu Buba ya caccaki gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed bisa dora laifin yunwa a kasar nan kan gwamnatin Bola Tinubu
  • Gwamnan Bauchi ya dora alhakin wahalar da ake sha a kasar nan kan manufofin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, wanda ya ce zai jawo gagarumar matsala
  • Amma Sanata Buba da ke wakiltar Bauchi ta Kudu, ya zargi gwamna Bala Mohammed da karkatar da motocin tallafin shinkafa daga jama'ar jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Bauchi - Sanata Shehu Buba da ke wakiltar Bauchi ta Kudu karkashin jam'iyyar APC ya yi kakkausan martani ga gwamnan jiharsa, Bala Mohammed.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya shiga matsala kan sukar Tinubu, an yi masa tonon silili

Musayar yawun na zuwa ne bayan gwamnan ya zargi gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da bullo da manufofin da su ka jawo zanga-zangar adawa da manufofinsa.

Bala Mohammed
Dan majalisar APC ya ba wa Tinubu kariya kan yunwa a Najeriya Hoto: Senator Bala AbdulKadir Mohammed/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa gwamna Bala Mohammed ya zargi manufofin gwamnatin tarayya da jefa talakawa cikin yunwa da matsi da kunci, wanda hakan ya jawo zanga-zanga.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Kai ne silar yunwa a Bauchi," Sanata

Sanata Shehu Buba ya mayarwa gwamnan Bauchi kalamansa na dalilan yunwa da fatara da kunci, inda ya zarge shi da jefa jama'ar Bauchi cikin mawuyacin hali, The Punch ta wallafa.

Sanatan ya kuma zargi gwamna Bala da karkatar da motar dawa guda 70, motar taki 70 da mota 20 ta shinkafa da gwamnatin Tinubu ta bayar a rabawa talakawan Bauchi.

Gwamnatin Bauchi ta yi martani

Gwamnatin jihar Bauchi ta yi martani ga sanata Shehu Buba kan cewa an handame kayan tallafi da gwamnatin tarayya ta aika jihar.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Tsohon gwamnan Kano ya gano bakin zaren, ya aika saƙo ga Tinubu

Mashawarcin gwamnan Bauchi kan yada labarai, Mukhtar Gidado ya ce babu kamshin gaskiya a zargin, kuma ana shirin raba abincin ga talakawa.

An zargi gwamnan Bauchi da gaza aiki

A baya kun ji labarin yadda tsohon kakakin majalisa, Yakubu Dogara ya soki gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed bisa kin yiwa jama'ar jiharsa aikin da zai cicciba rayuwarsu.

Rt Hon. Dogara, wanda dan asalin jihar Bauchi ne ya ce Sanata Bala Mohammed ba shi da hurumin sukar shugaba Bola Ahmed Tinubu domin babu abin da tabuka a jiharsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.