"Naira Miliyan 8.5 Ake Biya," Tsohon Dan Majalisa Ya Fallasa Kudin Gudanarwarsu duk Wata

"Naira Miliyan 8.5 Ake Biya," Tsohon Dan Majalisa Ya Fallasa Kudin Gudanarwarsu duk Wata

  • Tsohon dan majalisa daga shekarar 2015 zuwa 2023, Sergius Ogun ya bayyana kudin da ake biyansu a matsayin kudin gudanar da ofishin mazaba
  • Tsohon dan majalisar ya ce ana biyansu Naira Miliyan 8.5 duk wata domin tafiyar da harkokin ofishin mazabunsu da sauran al'amuran da su ka jibanci mazaba
  • Mista Sergius Ogun ya kara da cewa kila kudin gudanarwar tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ke magana a kai ba albashin wata-wata ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Ogun - Tsohon dan majalisa, Sergius Ogun ya bayyana cewa ana biyan kowannensu Naira Miliyan 8.5 duk wata a matsayin kudin gudanarwa.

Kara karanta wannan

"Ko mutum 1 ba a kashe a lokacin zanga zanga ba," Inji rundunar 'yan sandan Kano

Ya fadi haka ne bayan tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya caccaki yan majalisar kan kayyade albashinsu da kansu, lamarin da majalisar ta musanta.

Sergius Ogun
Tsohon dan majalisa ya ce N8.5bn ake biyansu duk wata domin gudanar da ofishin mazaba Hoto: Hon Sergius Ogun/Nigerian Senate
Asali: Facebook

Arise TV ta wallafa cewa Mista Sergius, wanda ya wakilci Esan ta Arewa-Gabas da Esan ta Kudu-Gabas a shekarar 2015 zuwa 2023, ya ce ana amfani da kudin ne wajen tafiyar da ofishin mazaba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ake amfani da kudin gudanarwar majalisa

Tsohon dan majalisar ya bayyana cewa ana amfani da Naira Miliyan 8.5 na kudin gudanarwa wajen sayen jaridu da tafiye-tafiye zuwa mazabun kowane dan majalisa da saukar baki.

A kan batun fita kasashen ketare, Hon. Ogun ya ce ba majalisa ce ta ke biyan kudin da ake ba 'yan majalisar na kula da kawunansu a kasashen wajen, Daily Trust ta wallafa.

Ya ce ana saya masu tikiti da kudin 'yan rakiya da na kula da kawunansu daga asusun gwamnati ba kudin gudanarwar da ake ba su duk wata ba.

Kara karanta wannan

'Yan majalisa sun fusata da kalaman Obasanjo, sun karyata zargin kayyade albashinsu

Obasanjo ya zargi majalisa da kayyade albashinsu

A wani labarin kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya zargi 'yan majalisun Najeriya da kayyadewa kansu albashin da su ke karba duk wata, wanda ya ce bai dace ba.

Tsohon shugaban ya yi zargin kowanne dan majalisar wakilai da ta dattijai ya karbi Naira Miliyan 200, kuma tuni su ka sanya hannu tare da karbe kudin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.