'Yan bindiga Sun Canza Salon Ta'addanci, Sun Budewa Motar Fasinjoji Wuta

'Yan bindiga Sun Canza Salon Ta'addanci, Sun Budewa Motar Fasinjoji Wuta

  • Wasu miyagun ƴan bindiga sun kai hari kan wasu matafiya a jihar Taraba da ke yankin Arewa maso Gabashin Najeriya
  • Ƴan bindigan sun hallaka fasinjoji bakwai tare da direbansu bayan sun buɗe musu wuta a hanyarsu ta zuwa Wukari
  • Mutanen dai dukkaninsu sun fito ne daga garin Takum, hedkwatar ƙaramar hukumar Takum a jihar ta Taraba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Taraba - Ana zaman ɗar-ɗar a garin Takum yayin da wasu ƴan bindiga suka kashe fasinjoji bakwai da direba a jihar Taraba.

Ƴan bindigan sun kashe fasinjojin ne a safiyar ranar Litinin a hanyar Takum zuwa Wukari a cikin jihar Taraba.

'Yan bindiga sun hallaka matafiya a Taraba
'Yan bindiga sun farmaki matafiya a Taraba Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Yadda ƴan bindiga suka kai harin

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ƴan bindigan sun farmaki mutanen ne a tsakanin garin Chanchangi na ƙaramar hukumar Takum da ƙauyen Saa’yi a jihar Benue.

Kara karanta wannan

An rasa rayuka, 'yan ta'addan Nijar sun yi wa sojoji kwanton bauna a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata majiya ta bayyana cewa ƴan bindigan sun buɗe wuta kan motar da ke ɗauke da fasinjojin, inda suka hallaka dukkanin mutanen da ke cikinta.

Majiyar ta ƙara da cewa ƴan bindigan waɗanda ake zargin sun fito ne daga dajin jihar Benue, ba su ɗauki komai ba daga cikin motar.

Hanyar dai ita ce wacce ƴan bindiga suka kashe Sarkin Chanchangi da babban ɗansa a cikin watan Yulin 2024.

Hanyar dai ta zama mai haɗarin gaske saboda yadda ƴan bindiga suke cin karensu babu babbaka wajen kai hari, yin garkuwa tare da fashi ga fasinjojin da ke wucewa cikin dare ko rana.

Me ƴan sanda suka ce kan harin?

Lokacin da aka tuntuɓi muƙaddashin kakakin rundunar ƴan sandan jihar Taraba, DSP Kwache Gambo, ta ce ba ta da masaniya kan harin.

DSP Kwace Gambo ta bayyana cewa za ta yi bincike domin gano haƙiƙanin abin da ya faru.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun ragargaji 'yan ta'addan Boko Haram a jihar Borno

Sojoji sun hallaka ƴan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun rundunar Birged ta shida sun samu nasarar hallaka ƙasurgumin ɗan bindigar da ake nema ruwa a jallo a Taraba.

Dakarun sojojin sashe na uku a rundunar Operation Whirl Stroke sun kashe ɗan ta'addan da ya addabi mutane a garuruwan da ke iyakar jihohin Taraba da Benue.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng