An Shiga Jimami a Arewacin Najeriya, Mata da Miji da ’Ya’yansu 5 Sun Mutu Bayan Cin Rogo

An Shiga Jimami a Arewacin Najeriya, Mata da Miji da ’Ya’yansu 5 Sun Mutu Bayan Cin Rogo

  • Wani magidanci, matsara da ƴaƴansu biyar sun sheka lahira bayan cin rogo a wani kauye a jihar Sokoto a Arewacin Najeriya
  • Mai unguwar kauyen, Muhammadu Modi ya bayyanawa manema labarai yadda cin rogo ya kashe iyalan gidan mutumin baki daya
  • Legit ta tattauna da likita, Dakta Zainab Rabi'u Abubakar kan jin yadda al'umma za su kare kansu daga shiga matsala a kan cin rogo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Sokoto - An shiga jimami bayan cin rogo ya hallaka mutane bakwai a garin Runjin Barmo a karamar hukumar Shagari a jihar Sokoto.

Rahotanni sun nuna cewa mutane bakwai ne yan gida daya suka mutu bayan cin abincin da aka yi da rogo a Sokoto.

Kara karanta wannan

Kisan kiyashi: Yadda maƙabartun Gaza suka cika ana birne gawa kan gawa

Sokoto
Iyalai bakwai sun mutu bayan cin rogo a Sokoto. Hoto: Legit
Asali: Original

Jaridar Aminiya ta wallafa cewa wani daga cikin wadanda suka ci rogon ya tsallaka rijiya ta baya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rogo ya kashe mata da miji da 'ya'ya

Rahotanni sun nuna cewa cin rogo ya jawo mutuwar iyalai har bakwai a karamar hukumar Shagari a jihar Sokoto.

Mutane bakwai din da suka mutu sun hada da mata da miji da ƴaƴansu guda biyar da ake zargin sun ci rogon.

Cin rogo: Mai unguwa ya yi magana

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Mai unguwar kauyen, Muhammadu Modi ya ce a ranar Laraba da ta wuce ne mutanen suka mutu.

Ya kuma tabbatar da cewa mutumin mai suna Malam Abubakar da matarsa mai suna Aisha sun mutu ne bayan cin abincin da aka hada da rogo.

Jami'an gwamnati sun yi magana

Kwamishinar lafiya ta jihar Sokoto, Asabe Balarabe ta ce za su gudanar da bincike domin tabbatar da hakikanin abin da ya jawo mutuwar mutanen.

Kara karanta wannan

Kwanaki 7 da addu'o'in talakawa, APC ta kiɗime, ta ba Sanatan da ya mutu muƙami

Ma'aikatar lafiya ta jihar ta dauki jinin mutumin da ya tsallake rijiya ta baya domin masa gwaje gwaje.

Cin rogo: Legit ta tattauna da likita

Wata likita a Asibitin Rasheed Shekoni da ke Dutse a jihar Jigawa, Zainab Rabi'u Abubakar ta ce yana da kyau kafin dafa rogo a jika shi sosai kamar na awa hudu domin rage gubar da yake cikinsa.

Sannan ta ce akwai hadari mutum yaci rogo danye a lokacin da yake jin yunwa wanda hakan na jawo tashin zuciya da amai ko rikewar numfashi wanda yana kaiwa ga mutuwa.

Yan ta'adda sun kai hari a Sokoto

A wani rahoton, kun ji cewa an rasa rayukan jami'an sojojin Najeriya bayan ƴan ta'adda sun yi musu kwanton ɓauna a ƙaramar hukumar Gudu a Sokoto.

Ƴan ta'addan sun hallaka sojoji huɗu tare da ƙona motocin sintiri biyu na jami'an tsaron a harin da suka kai a ranar Asabar da ta wuce a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng