Tinubu Ya Sanya Farin Ciki a Fuskar Daliban Jami’a, N20000 Ta Shiga Asusun Dalibai 20371

Tinubu Ya Sanya Farin Ciki a Fuskar Daliban Jami’a, N20000 Ta Shiga Asusun Dalibai 20371

  • Daliban da suka samu N20,000 daga asusun ba da lamunin karatu na NELFund sun nuna farin cikinsu kan alawus din Yuli da aka tura musu
  • Daliban dai sun fito ne daga jami'o'i shida da suka fara cin gajiyar tallafin NELFund, sun ce sun yi amfani da kudin wajen sayen kayan abinci
  • Matsalolin kudi babban kalubale ne da ke fuskantar yawancin daliban manyan makarantun gwamnati, abin da NELFund ke son magancewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Wasu daliban jami’o’i da suka ci gajiyar alawus din N20,000 da asusun ba da lamunin karatu na NELFUND ya biya, sun fara shagali bayan karbar kudin.

Yayin da wasu suka nuna mamakinsu a soshiyal midiya, an ce wasu daliban kuma sun fadi yadda suka sayi kayan abinci da kudin.

Kara karanta wannan

NNPC ke yiwa tattalin arziki zagon kasa? Kyari ya wanke kamfanin Najeriya

Daliban da suka samu alawus din Yuli daga NELFund sun sayi kayan abinci
Daliban da shirin NELFund ta biya alawus din Yuli sun yi farin ciki. Hoto: Frédéric Soltan/Getty Images, @officialABAT/X
Asali: UGC

Tinubu zai sharewa dalibai matsalar kudi

Matsalolin kudi babban kalubale ne da ke fuskantar yawancin daliban manyan makarantun gwamnati a Najeriya, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rashin kudi ya sa matasa da dama suka hakura da zuwa makaranta, saboda iyayensu ko masu kula da su ba za su iya daukar nauyin karatunsu na jami’a ba.

NELFund ta rabawa dalibai 20,371 kudi

Dalibai 20,371 daga manyan makarantu shida ne aka ce asusun NELFund ya turawa kowannensu N20,000 matsayin alawus din watan Yuli.

Jami'o'in da aka ce dalibansu sun ci gajiyar kudin sun hada da jami’ar Bayero da ke Kano; jami'ar tarayya ta Dutsin-Ma da ke Katsina.

Sauran sun hada da jami'ar Ilorin da ke Kwara; jami'ar Benin da ke Edo; jami'ar Ibadan da ke Oyo da jami'ar Maiduguri da ke Borno.

Kara karanta wannan

Yunwa na barazana ga rayukan almajiran Kano, an roki matasa su hakura da zanga zanga

Asusun NELFund ya fara raba kudin alawus ga daliban da hukumar ta riga ta biya musu kudin makaranta a ranar 5 ga Agusta, 2024.

Dalibai sun yi cefane da kudin NELFund

Wani dalibi dan aji uku a sashen aikin gona daga jami’ar Ibadan, Emmanuel John, ya shaida wa Sunday PUNCH cewa bai yarda zai samu kudin ba a lokacin da ya nema.

Ya ce:

“Na nemi rancen N240,000, domin a rika ba ni N20,000 duk wata. Na yi niyyar amfani da kudin domin sayen kayan abinci, da sauran wasu bukatu.

Wani dalibin 'lissafin kudi (akanta)' daga jami’ar Maiduguri, Muhammed Buba, ya ce ya yi mamaki da ya ga kudin, inda ya ce ya je kasuwa ya sayo kayan abinci nan take.

Shi kuwa wani dalibin 'sashen koyar da ilimi' na jami’ar Ilorin, Malik Ibrahim, ya ce da samun alawus din ya shirya shagalin biki tare da abokansa.

Kara karanta wannan

DSS ta warware rudanin da aka shiga bayan an kai samame ofishin NLC saboda zanga zanga

Malik ya ce da fari ya yi tunanin 'yan damfara ne suka tura masa sako saboda ya san N100 ce kadai ta rage a asusun bankinsa, inda ya yi godiya ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

NELFund: An rufe ba da rancen karatu

A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar kula da asusun ba da lamunin karatu (NELFund) ta dakatar da ba daliban manyan makarantun jihohi damar neman rancen kudin.

Hukumar ta sanar da dakatarwar wadda za ta dauki tsawon kwanaki 14 biyo bayan karancin daliban manyan makarantun jihohi da ke neman bashin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.