Gwamnan PDP Ya Shiga Matsala kan Sukar Tinubu, An Yi Masa Tonon Silili

Gwamnan PDP Ya Shiga Matsala kan Sukar Tinubu, An Yi Masa Tonon Silili

  • Tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, ya yi watsi da sukar da gwamnan jihar Bauchi ya yiwa Shugaba Bola Tinubu
  • Dogara ya bayyana cewa Gwamna Bala Mohammed ya kasa tsayawa ya yi abin da ya dace a jihar Bauchi
  • Ya yi zargin cewa jihar ta kasa samun wani kataɓus a cikin shekarun da gwamnan ya kwashe a kan karagar mulki

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Bauchi - Tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, ya caccaki gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed.

Yakubu Dogara ya caccaki gwamnan ne kan sukar da ya yiwa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Yakubu Dogara ya caccaki gwamnan Bauchi
Gwamna Bala ya soki salon mulkin Tinubu Hoto: Senator Bala Abdulkadir Mohammed, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Gwamna Bala Mohammed ya ɗora laifi kan Shugaba Tinubu bisa halin da tattalin arzikin ƙasar nan ke ciki a yanzu da kasa biyan buƙatun da masu zanga-zanga suka nema.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Tsohon gwamnan Kano ya gano bakin zaren, ya aika saƙo ga Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dogara ya faɗi laifin gwamnan Bauchi

Sai dai, Dogara wanda ɗan asalin jihar Bauchi ne ya ce gwamnan ba shi da hurumin sukar shugaban ƙasa ganin yadda ya gaza taɓuka abin kirki a matsayinsa na gwamna, cewar rahoton jaridar The Nation.

Ya bayyana cewa gwamnan ya nemi taimakon Tinubu bayan da ya murɗe zaɓe ya sake komawa kan kujerar gwamnan Bauchi a zaɓen 2023.

"Lokacin da Gwamna Bala Mohammed yake kotu bayan ya murɗe zaɓe sannan yana buƙatar Shugaba Tinubu ya cece shi, ya yi ta rera waƙoƙin yabo a gare shi."
"Ya yi ta gayawa duniya irin kirkin Tinubu ba tare da yin la'akari da cewa shi ne shugaban gwamnonin PDP ba."
"Ƴan watanni kaɗan bayan Shugaba Tinubu ya cece shi, ya koma yana bayyana shugaban ƙasan a matsayin wanda ba zai iya ba, wanda bai cancanci ya jagoranci Najeriya ba."

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP a Arewa ya shiga matsala kan sukar Tinubu, an gindaya masa sharuda

- Yakubu Dogara

Dogara ya caccaki Gwamna Bala

Dogara ya bayyana cewa shekara shida cikin mulkin gwamnan, har yanzu jihar Bauchi ba ta da abubuwan more rayuwa kuma tana ɗaya daga cikin jihohin da ke yawan yaran da ba su zuwa makaranta, rahoton Daily Post ya tabbatar.

Ya bayyana cewa duk da talaucin da jihar ke fama da shi a ƙarƙashin mulkinsa, gwamnan ya gina katafaren gidan gwamnati domin kansa da iyalansa da gidan iyalansa wanda ya fi kowane a Arewacin Najeriya ko ƙasa baki ɗaya.

An gargaɗi gwamnan Bauchi

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata kungiya a Arewacin Najeriya ta gargadi Gwamna Bala Mohammaed na jihar Bauchi kan kalaman da ya fito ya yi.

Kungiyar Arewa Young Leaders Forum (AYLF) ta yi gargadin ne bayan gwamnan ya yi shagube ga Bola Tinubu kan zaben 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng