Dakarun Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Ta'addan Boko Haram a Jihar Borno

Dakarun Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Ta'addan Boko Haram a Jihar Borno

  • Dakarun sojojin Najeriya masu yaƙi da ƴan ta'adda a jihar Borno sun samu nasarar hallaka ƴan ta'addan Boko Haram
  • Dakarun sojojin sun hallaka ƴan ta'adda mutum biyar a wani samame da suka kai musu a maɓoyarsu da ke ƙaramar hukumar Bama ta jihar
  • Jami'an tsaron sun kuma ƙwato makamai masu tarin yawa daga hannun masu tayar da ƙayar bayan da suka addabi jama'a

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar kashe ƴan ta'addan Boko Haram mutum biyar a jihar Borno.

Dakarun sojojin sun samu nasarar ne a kan ƴan ta'addan a wani samame da suka kai maboyarsu a jihar.

Sojoji sun hallaka 'yan ta'adda a Borno
Dakarun sojoji sun hallaka 'yan ta'adda a Borno Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Facebook

Sojoji sun hallaka ƴan Boko Haram

Kara karanta wannan

Atiku ya sake yin gargadi kan kawo cikas ga matatar man Dangote, ya ba da shawara

Masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama ya bayyana hakan a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zagazola ya ce dakarun sojojin na Operation Hadin Kai sun kashe ƴan ta'addan ne a wani farmaki da suka kai a dajin Sambisa.

Dakarun sojojin tare da hadin gwiwar rundunar haɗin gwiwa, sun gudanar da wani samame a ranar Asabar a yankin ƴan ta'addan dake ƙaramar hukumar Bama ta jihar.

A cewar Zagazola Makama, wata majiyar sirri ta bayyana cewa, a yayin farmakin, wasu ƴan ta'addan sun gudu yayin da aka kashe biyar daga cikinsu.

Sojojin sun ƙwato makamai da suka haɗa da bindigogi ƙirar gida guda uku, bama-baman RPG guda biyu, cajar RPG guda ɗaya, jigida guda ɗaya, harsasai guda 23 masu kaurin 7.62 x 54mm da ƙwayoyi.

Sojoji na samun nasara kan ƴan Boko Haram

Kara karanta wannan

Daga karshe 'yan sanda sun bayyana dalilin kai samame a hedkwatar kungiyar NLC

Wannan ci gaban shi ne na baya-bayan nan a yaƙin da sojoji ke yi da masu tayar da ƙayar bayan

A ranar 9 ga watan Agusta, sojoji sun kashe ƴan ta'addan Boko Haram 14 a wani samame da suka kai a maɓoyarsu da ke a Bula Dalo, Bula Marwa, Gaizuwa, da Chongolo a ƙaramar hukumar Bama ta jihar.

Sojoji sun ragargaji ƴan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun rundunar sojojin Najeriya sun yi musayar wuta da wasu yan bindiga a ƙananan hukumomin jihar Kaduna.

Dakarun sojojin sun samu gagarumar nasara kan miyagun ne bayan sun yi musayar wuta inda suka sheƙe mutum biyu daga cikinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng