Gwamnatin Katsina Ta Dauki Matakin Tausayawa Talakawa Sakamakon Zanga Zanga

Gwamnatin Katsina Ta Dauki Matakin Tausayawa Talakawa Sakamakon Zanga Zanga

  • Gwamnatin jihar Katsina ta ɗauki matakin sake sassauta dokar hana fita da ta sanya a faɗin jihar biyo bayan zanga-zanga
  • Muƙaddashin gwamnan jihar, Faruk Lawal Jobe ya mayar da dokar hana fitan daga ƙarfe 10:00 na dare zuwa ƙarfe 5:00 na safe
  • Faruk Jobe ya yabawa jama'a bisa haɗin kan da suka ba da sannan ya shawarci da su ci gaba da bin doka da oda

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Gwamnatin jihar Katsina ta sake sauƙaƙa dokar hana fita da ta sanya a jihar.

Dokar ta hana zirga-zirga daga ƙarfe 7:00 na dare zuwa karfe 7:00 na safe yanzu an mayar da ita daga ƙarfe 10:00 na dare zuwa ƙarfe 5:00 na safe a faɗin jihar.

Kara karanta wannan

Ana shirin gama zanga zanga, gwamna ya sake daukar sabon mataki

Gwamnatin Katsina ta sassauta dokar hana fita
Gwamnatin Katsina ta sake sassauta dokar hana fita Hoto: Ibrahim Kaulaha Muhammad
Asali: Facebook

Sakataren gwamnatin jihar, Abdullahi Faskari, a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun daraktan yaɗa labaransa Abdullahi Yar’adua ya bayyana hakan a ranar Asabar, cewar rahoton tashar Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa gwamnati ta sassauta dokar?

Sanarwar ta bayyana cewa muƙaddashin gwamnan jihar, Faruk Jobe ya gamsu da rahotannin da ake samu na ingantar harkokin tsaro a faɗin jihar, rahoton Daily Post ya tabbatar.

Hakan ya sanya ya ba da umarnin sake yin duba kan dokar hana fitan ba tare da ɓata lokaci ba.

Faruk Jobe ya yaba da yadda jami'an tsaro ke gudanar da ayyukansu da kuma haɗin kan da jama'a suka ba da yayin da gwamnati ke ƙoƙarin shawo kan lamarin.

Ya shawarci al’ummar jihar da su ci gaba da bin doka da oda domin ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum.

Kara karanta wannan

An shiga jimami bayan jirgi dauke da fasinjoji ya kone, an rasa rayukan mutum 20

An sanya dokar hana fitan ne sakamakon rikicin da ya ɓarke a zanga-zangar #EndBadBadGovernance a jihar.

Matakin ya yi daidai

Wani mazaunin jihar Katsina, Muhammad Auwal ya gayawa Legit Hausa tabbas matakin na sake sassauta dokar ya yi abin a yaba ne.

Ya bayyana cewa al'amura sun daidaita kuma hankula sun kwanta biyo bayan hargitsin da aka samu sakamakon zanga-zangar.

"Eh matakin abin a yaba ne domin jama'a za su ƙara samun sauƙi wajen gudanar da harkokinsu na yau da kullum."

- Muhammad Auwal

Gwamnatin Plateau ta sassauta dokar hana fita

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Plateau ta sake sassauta dokar hana fita da ta sanya a Jos-Bukuru sakamakon ɓarnar da ta biyo bayan zanga-zangar da aka yi.

Hakan ya biyo bayan ingantuwar yanayin tsaro a yankunan da kuma yadda mutane suka bi dokar hana fitan sau da ƙafa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng