Kano: Dan Majalisa Ya Magantu Kan Farmaki Yayin Taro da Aminu Ado Ya Halarta
- Dan Majalisar jihar Kano daga jam'iyyar NNPP, Hon. Abdul-Majid Umar ya bayyana yadda ya tsira da rayuwarsa yayin taron saukar Alkur'ani
- Hon. Umar ya ce matasa da dama sun yi ta zaginsa da kuma jifansa yayin taron wanda Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya halarta
- Wannan na zuwa ne bayan farmaki da matasa suka kai kan dan Majalisar kan zargin hadin baki wurin rushe masarautun Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Dan Majalisar jihar Kano, Hon. Abdul-Majid Umar ya yi magana kan yadda ya sha da kyar yayin taro da Aminu Ado Bayero ya halarta.
Dan Majalisar da ke wakiltar mazabar Gwale ya nuna damuwa kan yadda ya kadu da tsallake rijiya ta baya yayin taron saukar Alkur'ani.
Kano: Hon. Umar ya zargi Gwamnatin Tarayya
Hon. Umar ya bayyana haka a hira da jaridar Leadership inda ya koka kan yadda mutane suka kai masa hari yayin taron a jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da Majalisar ya zargi Gwamnatin Tarayya da kara ruruta riciki bayan matakin da Majalisar jihar ta dauka na rusa masarautun.
Hon. Umar ya bayyana yadda wani daga cikin masu gadin sarkin Kano na 15, Aminu Ado ya daga hannu domin buge shi a taron, cewar Premium Times.
Yadda dan Majalisa ya sha da kyar
"Na zauna kusa da Aminu Ado lokacin da ya zo taron inda wasu na kusa da shi suka fara cin mutunci na da zagi."
"Sun zazzage ni saboda zargin ina daga cikin wadanda suka amince da dokar rushe masarautun jihar da Majalisar ta yi."
"Dalilin haka ya sanya dole na bar wurin taron cikin gaggawa saboda yadda mutane ke neman kai farmaki gare ni."
- Hon. Abdul-Majid Umar
Hon .Umar ya ce matasa da dama na dauke da makamai tare da jifansa inda 'yan sanda suka tseratar da shi daga harin.
An gudanar da addu'o'i a Kano
Kun ji cewa wasu mazauna jihar Kano sun gudanar da addu'o'i da salloli saboda halin kunci da ake ciki.
An gudanar da karatuttukan Alkur'ani mai girma da kuma addu'o'i a wurare daban-daban a fadin jihar Kano.
Asali: Legit.ng