Atiku Ya Sake Yin Gargadi Kan Kawo Cikas Ga Matatar Man Dangote, Ya Ba da Shawara
- Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya yi gargaɗi kan duk wani yunƙuri da ake yi na kawo cikas ga ci gaban matatar man Dangote
- Atiku Abubakar ya kuma yi kira ga ƴan Najeriya da gwamnati mai ci da su bayar da cikakken goyon baya ga matatar man Dangote
- Kalaman Atiku sun zo ne a matsayin martani kan rikicin da ke faruwa tsakanin matatar man Dangote da hukumar NMPDRA kan batun rabon ɗanyen mai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya yi gargadi kan yunkurin da ake yi na ganin bayan matatar man Dangote da gangan.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya bayyana cewa matatar man Dangote za ta iya warware matsalar ƙarancin man da ake fama da ita a ƙasar nan da samar da isassun kuɗaɗen ƙasashen waje.
Atiku ya yi waɗannan kalaman ne a shafinsa na X a ranar Asabar, 10 ga watan Agustan 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kalaman na sa na zuwa ne yayin da yake martani kan taƙaddamar da ke tsakanin matatar man Dangote da hukumar NMPDRA kan batun samar da ɗanyen mai ga matatar.
Atiku ya buƙaci a goyawa matatar man Dangote baya
Da yake bayyana matatar a matsayin zuwan jariri, Atiku ya buƙaci ƴan Najeriya da gwamnati mai ci su goyi bayan matatar domin ganin ta samu nasara.
"Duk mahaifin da yake jiran samun jariri zai ɗauki dukkanin matakan da suka dace domin tabbatar da cewa kula da wannan ƙaruwar da ya samu ta zama abin da ya fi mayar da hankali a kai."
"Wannan tsarin haka yake a wajen zuba hannayen jari, na cikin gida na ko na ƙasashen waje."
"Bisa wannan fahimtar, ina taka tsan-tsan wajen yin la'akari kan duk wani yunƙuri na gangan domin kawo cikas ga ci gaban matatar man Dangote."
"Tare da sauran ƴan ƙasa, ina kira ga dukkanin ƴan Najeriya da su ɗauki matakai domin samun tabbaci cewa wasu daga ciki ko wajen ƙasar nan ba su haɗa kai ba domin hana mu cin gajiyar wannan matatar da muka daɗe muna jira."
- Atiku Abubakar
Matatar man Dangote za ta kawo cikas
A wani labarin kuma, kun ji cewa cewa babbar matatar man duniya da aka gina a Najeriya mallakin attajiri Aliko Dangote za ta kawo cikas ga harkar mai a Turai.
An bayyana cewa matatar man Dangote za ta zama tamkar kadangaren bakin tulu ga Turai musamman ma masana'antar mai da gas a Arewa maso Yammacin Turai (NWE).
Asali: Legit.ng