Bayan Sake Kai Ganduje Kara, APC Ta Yi Sabon Zargi Kan Gwamnatin Abba a Kano
- Jam'iyyar APC ta yi zargin cewa wasu daga cikin jami'an gwamnatin jihar Kano sun karkatar da shinkafar da gwamnatin tarayya ta kawo a jihar
- Shugaban jam'iyyar na jihar ya buƙaci a gudanar da bincike kan zargin karkatar da tallafin na gwamnatin tarayya
- Abdullahi Abbas ya kuma yi zargin cewa gwamnatin na ɗaukar ayyukan gwamnatin tarayya a matsayin na ta duk da ba ita ta yi su ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Jam’iyyar APC ta buƙaci a gudanar da bincike kan zargin karkatar da shinkafar da gwamnatin tarayya ta ba gwamnatin jihar Kano da wasu jami’ai suka yi.
Jam’iyyar ta kuma buƙaci da a gaggauta gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kwamitin bincike mai zaman kansa.
Wane zargi APC ta yi?
Shugaban jam’iyyar APC na jihar, Alhaji Abdullahi Abbas, ya nuna damuwarsa kan yadda wasu jami’an gwamnatin NNPP suke ci gaba da karkatar da kayan tallafin da ake bayarwa, cewar rahoton jaridar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya yi gargadin cewa rashin ɗaukar matakin da ya dace zai sanya a kalli hakan a matsayin goyon baya ga waɗannan munanan ayyuka na rashin kishin ƙasa, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.
Abdullahi Abbas ya buga misalai da dama kan inda aka ga shinkafar ta gwamnatin tarayya, ciki har da makarantar Sagagi.
Shugaban na APC ya kuma zargi gwamnatin da sauya buhunan kayan tallafin da hoton Gwamna Abba da tambarin NNPP domin siyarwa ga ƴaƴan jam'iyyar NNPP.
Abdullahi Abbas ya kuma caccaki gwamnatin bisa yadda take cewa ita ce ta yi ayyukan da gwamnatin tarayya ta yi, irinsu rabon taki da iri ga manoma.
Gwamnati ta yi martani
Da aka tuntuɓi shugaban ma'aikatan gwamnan jihar, Shehu Sagagi, ya musanta zargin cewa ya karkatar da shinkafar da gwamnatin tarayya ta ba da domin a rabawa mutanen jihar.
"Shinkafar da aka gani a makarantar Islamiyyata, wacce na siya ce da kuɗina ko wasu suka bayar da sadakarta."
"Na daɗe ina da ɗabi'ar ciyar da yara a makarantar Islamiyyata, wanda tun kafin na zama shugaban ma'aikatan gwamna na ke yin hakan."
- Shehu Sagagi
Gwamnatin Tinubu ta dakatar da siyar da shinkafa
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu ta dakatar da shirin siyar da shinkafa mai nauyin kilo 50 ga ƴan Najeriya.
Tun da farko gwamnatin ta so tallafawa ma'aikata ne domin samun shinkafar cikin farashi mai rahusa kan N40,000 kacal.
Asali: Legit.ng