'Yan Sanda Sun Bayyana Dalilin Kasa Cafke 'Yan Bindigan da Ke Nuna Kansu a Duniya
- Kakakin rundunar ƴan sandan Najeriya ya yi martani kan wani hoton ƴan bindiga da aka sanya suna kuɗaɗen fansar da suka karɓa
- Muyiwa Adejobi ya bayyana cewa ƴan sanda ba za su iya cafƙe dukkanin masu laifi ba a lokaci ɗaya amma suna kama da yawa daga cikinsu
- Ya buƙaci jama'a da su riƙa yabawa ƙoƙarin da jami'an tsaro ke yi wajen samar da tsaro da zaman lafiya a ƙasar nan
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Kakakin rundunar ƴan sandan Najeriya, Muyiwa Adejobi, ya yi martani kan wani hoton ƴan bindiga da ke nuna kuɗaɗen fansar da suka karɓa.
Kakakin rundunar ƴan sandan ya bayyana cewa suna bakin ƙoƙarinsu amma ba za su iya cafke dukkanin masu laifi a lokaci ɗaya ba.
Ƴan bindiga na cin karensu babu babbaka
Muyiwa Adejobi ya yi martani ne dai kan wani hoto da Zagazola Makama ya sanya a shafinsa na X wanda ya nuna ƴan bindiga ɗauke da kuɗaden fansa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zagazola Makama ya bayyana cewa yanzu ƴan bindiga ko tsoro ba su ji wajen fitowa su nunawa duniya irin bushashar da suke yi.
Da yake martani kan hoton a shafinsa na X, Muyiwa Adejobi, ya bayyana cewa jami'an tsaro suna yin bakin ƙoƙarinsu wajen ganin cewa an samu tsaro a ƙasar nan.
Ƴan sanda sun yi kira ga jama'a
Ya buƙaci jama'a da su riƙa yabawa da ƙoƙarin da jami'an tsaro suke yi wajen tabbatar da tsaro a ƙasar nan.
Kakakin ya bayyana cewa tabbas ba za su iya cafke dukkanin masu laifi a lokaci ɗaya ba, amma babu mai laifin da ba zai fuskanci hukunci ba.
"Ba zamu iya cafke dukkanin masu laifi ba a lokaci ɗaya. Aƙalla a yaba mana kan waɗanda muka kama. A kullum muna kama da yawa daga cikinsu."
"Sojoji da ƴan sanda na yin iyakar baƙin ƙoƙarinsu. Ya kamata a riƙa yabawa kan ƙoƙarin da jami'an tsaro ke yi."
"Ya kamata mu haɗa kai domin magance matsalar rashin tsaro da sauran laifuka a Najeriya. Abu ɗaya da na tabbatar shi ne, babu mai laifin da ba zai fuskanci hukunci ba. Nagode."
- Muyiwa Adejobi
Dalilin ƴan sanda na zuwa hedkwatar NLC
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sandan Najeriya ta bayyana cewa jami’anta sun bi sahun wani wanda ake zargi zuwa wani shago a ginin ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC).
Rundunar ta bayyana cewa ta je ofishin ne domin cafke wani ɗan kasar waje da ke da hannu wajen aikata laifuka da dama a faɗin Najeriya da sauran ƙasashen Afirika.
Asali: Legit.ng