An Gano Mutane 19 da Suka Mutu Sakamakon Mummunan Haɗarin Jirgi

An Gano Mutane 19 da Suka Mutu Sakamakon Mummunan Haɗarin Jirgi

  • Rahotanni daga jihar Bayelsa sun nuna cewa an yi nasarar tsamo gawarwakin fasinjoji 19 daga teku bayan haɗarin jirgin ruwa
  • Tun ranar Laraba da ta gabata wani jirgin ruwa da ya ɗauko ƴan kasuwa galibi mata da kayansu ya kama da wuta a hanyar zuwa Yenagoa
  • Yanzu haka dai an kai gawarwakin waɗanda suka mutu ɗakin ajiyar gawa da ke babban asibitin tarayya FMC a babban birnin jihar Bayelsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bayelsa - Rahoto ya nuna zuwa yanzu an tsamo gawarwaki 19 daga kogin Ezetu 1 da ke karamar hukumar Ijaw ta kudu a jihar Bayelsa biyo bayan hadarin jirgin da ya afku.

Idan baku manta ba mun kawo muku rahoton yadda wani jirgin ruwa ɗauke da ƴan kasuwa galibi mata da kayansu ya gamu da ibtila'i a ranar Laraba da ta wuce.

Kara karanta wannan

Gwamna a Arewa ya taso masu zanga zanga a gaba, ya yi kakkausan kashedi

Taswirar jihar Bayelsa.
Jami'ar da yan su sun tsamo gawarwakin mutum 19 bayan haɗarin kwale-kwale a Bayelsa Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Kwale-kwale ya kama da wuta a Bayelsa

An ce Kwale-kwalen ya taso ne daga yankin Ekeni inda injinsa ya kama wuta a Unguwar Ezetu I da ke gabar Tekun Atlantika da misalin karfe 3 na rana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda Daily Trust ta kawo a rahoto, jirgin yana kan hanyar zuwa Swali a Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa lokacin da injin ya kama da wuta ya fashe.

Kawo yanzu an gano gawarwakin mutane 19 daga cikin waɗanda ke cikin kwale-kwalen yayin da ƴan su da ƴan sandan ruwa ke ci gaba da aikin ceto, in ji rahoton Vanguard.

Jami'an ceto sun ciro mutum 19

Bayanai sun nuna tun jiya da daddare aka kai gawarwakin mutun 16 ɗakin ajiye gawa na asibitin tarayya FMC da je Yenagoa yayin da safiyar Asabar aka kai wasu uku.

Kwamishinan Ma’aikatar Ruwa da Tattalin Arziki, Dokta Faith Zibs-Godwin, tare da wasu manyan jami’an gwamnati ne suka karɓi gawarwakin a caji ofis na ƴan sandan ruwa kusa da FMC.

Kara karanta wannan

Kaico: Ƴan bindiga sun hallaka basarake, sun yi awon gaba da mata da ƙananan yara

Shugaban kungiyar ma’aikatan ruwa na jihar Bayelsa, Ipigansi Ogoniba wanda ya zanta da manema labarai ya tabbatar da tsamo gawarwakin mutane 19 kawo yanzu.

Jirgin sama ya faɗo a Brazil

A wani labarin kuma wani jirgin sama ɗauke da fasinjoji 62 ya yi haɗari a kusa da Sao Paulo a kasar Brazil ranar Jumu'a, 9 ga watan Agusta, 2024.

Rahotanni sun bayyana jirgin ya faɗo ne a kusa da wani gida kuma ya kama da wuta, inda duka mutane 62 da ke ciki suka mutu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262