Ranar Ƙarshe: Masu Zanga Zanga Sun Sake Fantsama Kan Tituna, Ƴan Sanda Sun Ankara
- Masu zanga zanga sun sake tururuwa a kan tituna a babban birnin tarayya Abuja yau Asabar, 10 ga watan Agusta, 2024
- Tuni dai ƴan sanda suka ƙara tsaurara tsaro a kwaryar birni tun ranar Jumu'a saboda masu zanga-zanga na shirin rufewa da gagarumin tattaki
- Da misalin karfe 7:00 na safiya matasa suka fito zanga-zanga ta ƙarshe a Abuja kamar yadda suka tsara tun farko
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Bayan lafawa na ɗan taƙaitaccen lokaci, masu zanga zanga sun sake komawa kan tituna a birnin tarayya Abuja yau Asabar, 10 ga watan Agusta. 2024.
Zanga-zangar wacce a baya aka dakatar da ita saboda samamen da jami'an tsaro suka kai gidaje da kame masu jagorantar zanga-zangar, yanzu haka tana ci gaba da gudana.
Jaridar Punch ta tattaro cewa a ranar 1 ga watan Augusta, 2024 ƴan Najeriya suka fara zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa kuma a yau ake sa ran karkare ta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar yadda suka tsara tun farko, zanga-zangar za ta ɗauki tsawon kwanaki 10 kuma a yau jagororin da suka shirya gagarumin tattaki na mutane miliyan 1 a faɗin Najeriya.
Ƴan sanda sun ɗauki mataki
Domin shiryawa wannan gagarumin tattaki, tun ranar Jumu'a hukumomi suka girke dakarun tsaro a kewayen musamman wurare a kwaryar birnin Abuja.
Haka kuma a dandalin Eagles Square, an samu karuwar adadin jami’an tsaro da ke jibge a wurin saboda zanga-zangar ranar ƙarshe, Daily Trust ta rahoto.
Wannan dai wani sauyi ne wanda ba a ga irinsa ba a kwanaki uku da suka gabata, kwanakin da masu zanga-zanga suka huta ba su fito kan tituna ba.
Masu zanga-zanga sun tura saƙo
A yau Asabar, masu zanga-zangar, wadanda suka fara fitowa tun da karfe 7 na safe, sun yi ta maimaita "a kawo karshen yunwa" da "A dawo mana da tallafin man fetur," da dai sauransu.
Polan ta roki Njeriyata sakin ƴan ƙasarta
A wani rahoton kuma ƙasar Poland ta roƙi Najeriya ta haƙura da saki ƴan ƙasarta da aka kama da laifin ɗaga tutocin Rasha lokacin zanga-zanga a Kano.
Mataimakin ministan harkokin wajen ƙasar, Jakub Wisniewski ya ce ƴan Poland bakwai da aka kama sun aikata laifin ne cikin jahilci.
Asali: Legit.ng