Musulmai Sun Roki Alfarma, a Cire Ruwa a Tallafin N110bn da Za a Rabawa Matasa

Musulmai Sun Roki Alfarma, a Cire Ruwa a Tallafin N110bn da Za a Rabawa Matasa

  • Aminu Abdullahi Chubado ya yi tir da yadda aka cusa riba a cikin tallafin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu
  • Za a ba matasa tallafin N110bn domin bunkasa kasuwanci a Najeriya, amma ana tsoron akwai riban 5% a ciki
  • Chubado wanda ‘dan kasuwa ne a garin Kano ya yi korafi cewa Musulman kirki ba za su iya cin gajiyar tallafin ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Wasu musulmai masu kishin addininsu sun yi kira da babbar murya ga gwamnatin tarayya kan batun bashi da ruwa.

Wani dalibin ilmi kuma ‘dan kasuwa, Aminu Abdullahi Chubado ya koka a kan yadda aka sa ruwa a tallafin NYIF da za a ba matasa.

Bola Tinubu
Musulmai na so gwamnatin Bola Tinubu ta cire ruwa a tallafin NYIF Hoto: @BayoOnanuga1956
Asali: Twitter

Ruwa ya hana matashi neman tallafi

Kara karanta wannan

'Dawo da tallafin mai a ɓoye': Jigon PDP ya buƙaci Tinubu ya faɗa wa yan Najeriya gaskiya

Malam Aminu Chubado ya bayyana kokensa a dandalin X watau Twitter, yake cewa yake cewa riba ta hana shi neman tallafi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan za a tuna, Nairametrics ta ce gwamnati ta kawo wani tsarin agazawa matasa da jarin N110bn domin a iya bunkasa kasuwancinsu.

Bashi da ruwa a tallafin NYIF

Sai dai matashin ya bayyana cewa akwai ruwan 5% a kan wannan bashi da ‘dan kasuwa zai kara idan har ya tashi biyan bashin.

Da mu ka zanta da shi, Mal. Chubado ya bayyana cewa za su so gwamnatin Bola Tinubu ta cire ruwan da ya zama takunkumi gare su.

“Na so in nemi tallafin jarin matasa na kasa, sai na duba ka’idoji da sharudan bashin, sai na lura akwai ruwan kasha 5%.
Bayan cika duka sharudan, ba zan iya neman bashin ba, saboda kurum akwai ruwa. Ya kamata zababbun wakilanmu su yi wani abin a kan wannan.

Kara karanta wannan

Tinubu zai fitar da N280bn: An shirya karasa gina kilomita 82 na babban titin Arewa

- Aminu Abdullahi Chubado

Musulunci ya haramta bashi da ruwa

A cewar ‘dan kasuwar, malaman musulunci sun nuna rashin halaccin karbar irin duka wadannan bashi kamar na su NIRSAL.

Ganin mafi yawan malamai sun ce haramun ne cin bashi da ruwa, ‘dan kasuwan ya roki shugabanni su kawo tsarin musulunci.

Ana so 'yan majalisa su cire ruwa

Legit ta lura tuni aka fara yin kira ga ‘yan majalisu irinsu Bello El-Rufai su yi yunkuri a majalisa domin a musuluntar da bashin.

A dandalin na X, wani Shamsudden Sulaiman Jere ya jawo hankalin mai girma Kashim Shettima da Barau Jibrin kan batun.

Ganin Ministar matasa musulma ce, an yi kira a gare ta cewa a cire ruwan da aka kakaba wajen ba da wannan tallafin kasuwanci.

Duk da ana mulki a karkashin tikitin musulmi da musulmi, Muhammad Karamba ya ce ba a la’akari da addini a tsarin tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: abin da Ministan Tinubu ya fadawa Sanusi II da miyagu suka lalata cibiyar NCC

Ana so gwamnati ta kama 'Dan Bello

Ana da labari Bello Habib Galadanci watau Dan Bello yana taba kowa, amma Bashir El-Rufai ya gargade shi da sukar masu mulki.

Dan Bello ya na ganin yana wayar da kan jama’a ne, amma wasu su na zargin yana kawo abubuwan da babu gamsassun hujjoji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng