Mutane 62 Sun Mutu Yayin da Jirgin Sama Ya Yi Mummunan Haɗari, Bidiyo Ya Fito
- Wani jirgin sama ɗauke da fasinjoji 62 ya yi haɗari a kusa da Sao Paulo a kasar Brazil ranar Jumu'a, 9 ga watan Agusta, 2024
- Rahotanni sun bayyana jirgin ya faɗo ne a kusa da wani gida kuma duka mutane 62 da ke ciki sun mutu
- Bidiyoyin da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda jirgin ya faɗo ƙasa ba zato ba tsammani
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Sao Paulo, Brazil - Wani jirgin sama da ya ɗauko fasinjoji 62 ya yi haɗari ranar Jumu'a, 9 ga watan Agusta, 2024 a kusa da birnin Sao Paulo na kasar Brazil.
Rahotanni sun nuna cewa jirgin ya taso ne daga filin sauka da tashin jiragen sama na Cascavel da nufin zuwa Sao Paulo amma ya faɗo a kusa da wani gida.
Brazil: Fasinjoji nawa ne a jirgin?
A rahoton da BBC ta tattaro, duka fasinjoji 62 da jirgin ya ɗauko sun mutu sakamakon hatsarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamfanin sufurin jiragen sama na VoePass, masu jirgin da ya yi hatsarin sun bayyana cewa ya ɗauko mutane 58 da ma'aikata huɗu, a cewar rahoton APN News.
Al Jazeera ta ruwaito cewa gida daya ne kaɗai da ke wajen birnin Sao Paulo ya lalace a yankin da jirgin ya fado amma babu daya daga cikin mazauna wurin da ya jikkata.
Yadda jirgin ya faɗo a Sao Paulo
Wani faifan bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta ya nuna jirgin yana jujjuyawa a lokacin da ya yo ƙasa kafin daga bisani ya faɗi.
Lamarin dai ya haifar da wata babbar gobara, inda hayaki ya turnuke daga wani abu da ake ganin kamar tulun jirgin ne a kusa da gidajen da al'umma ke ciki a gefen birni.
Shugaban Brazil ya yi ta'aziyya
Shugaban kasar Brazil, Luiz Inacio Lula da Silva, ya bayyana cewa da alama dukkan mutanen da ke cikin jirgin sun mutu.
"Labari mara daɗi, ina jajanta wa iyalai da abokan wadanda ibtila'in ya rutsa da su," in ji shi.
An yi mummunan hatsarin mota a Zaria
A wani rahoton kuma jama'a sun shiga tashin hankali a yankin Gwargwaje, a karamar hukumar Zaria bayan motoci biyu sun yi karo da juna.
Shugaban hukumar kare afkuwar hadurra a Kaduna, Kabir Nadabo ya bayyana cewa mutum 11 sun rasu nan take.
Asali: Legit.ng