Sarauta Ta Kare: Kotu Ta Daure Basarake Shekaru 3 a Gidan Kaso, Ta Ci Tararsa

Sarauta Ta Kare: Kotu Ta Daure Basarake Shekaru 3 a Gidan Kaso, Ta Ci Tararsa

  • Wani basarake ya gamu da tsautsayi inda kotun magistare ta daure shi shekaru uku a gidan kaso a jihar Ondo
  • Basaraken mai suna Francis Ogundeji ya shiga matsala bayan saba umarnin kotu a lokuta da dama a jihar
  • Ana zargin Ogundeji da karkatar da wasu filaye da kotun ta yi umarnin dakatar da siyar da su amma ya yi biris da ita

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ondo - Kotun Magistrate da ke jihar Ondo ta daure basarake mai daraja a gidan kaso.

Kotun da ke zamanta a Ogbokoda ta daure basaraken mai suna Francis Ogundeji shekaru uku

An daure basarake shekaru 3 a gidan kaso
Kotu ta daure basarake a jihar Ondo shekaru 3 a gidan gyaran hali. Hoto: Legit.
Asali: Original

Ondo: Zargin da ake yi wa basaraken

Kara karanta wannan

Kaduna: Motar golf ta yi taho mu gama da gingimari, ana tsoron dukkanin fasinjoji sun mutu

Punch ta tattaro cewa Ogundeji shi ke sarautar yankin Ebute Ipare a karamar hukumar Ilaje a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana zargin basaraken da saba ka'ida da kuma kin bin umarnin da kotu a jihar Ta bayar, cewar TheCable.

Alkalin kotun, Mai Shari'a, E.A Manuwa shi ya yanke hukuncin a farkon wannan mako da muke ciki.

Alkalin kotun ya ce ana zargin Ogundeji da hada baki wurin siyar da wani fili tun a shekarar 2022 da muke ciki.

Ya ce kotu ta ba da umarninkan filin amma suka yi biris da ita inda suka lallaba suka siyar wanda hakan ya sabawa dokar kasa.

Hukuncin kotu kan basaraken a Ondo

Har ila yau, ana zarginsu da zamba da damfara inda suka sauya kwanan wata da ke jikin takardar filin.

Daga bisani, an same su da laifuffuka da suka saba doka inda aka daure su shekaru uku rare da zabin biyan tara daya N150,000.

Kara karanta wannan

Gwamna a Najeriya ya dage takunkumi kan basarake mai daraja bayan mummunan zargi

Gwamna ya dawo da basaraken sarauta

Kun ji cewa Gwamnatin jihar Oyo ta janye takunkumin da ta kakaba kan wani fitaccen basarake a jihar bayan dakatar da shi na tsawon lokaci.

Gwamnatin jihar da janye dakatarwar ne kan basaraken na Ido, Oba Gbolagade Babalola bayan dakatar da shi na watanni shida.

Adeojo ya bayyana haka ne yayin mika takardar dawo da basaraken inda ya taya shi murnar samun dawowa kan sarauta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.