'Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Babban Malamin Addinin Musulunci a Arewacin Najeriya

'Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Babban Malamin Addinin Musulunci a Arewacin Najeriya

  • Ƴan bindiga sun kutsa kai cikin gida, sun yi awon gaba da babban malamin addinin Musulunci Sheikh Isma'il Gausi a Zaria da ke jihar Kaduna
  • Wata majiya daga yankin ta bayyana cewa ƴan bindigar sun yi harbe-harbe domin tsorata mutane kafin su tafi da malamin ranar Laraba
  • Majiyar ta yi kira ga mahukunta su yi bakin ƙoƙarinsu wajen kubutar da malamin daga hannun miyagu cikin ƙoshin lafiya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zaria, jihar Kaduna - Wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da babban malamin addinin Musulunci, Sheikh Isma’il Gausi, a Zaria da ke jihar Kaduna.

Rahotanni sun bayyana cewa ƴan ta'addan sun yi harbe-harbe domin tsorata mutane kafin daga bisani su tasa malamin zuwa wurin da ba a sani ba.

Kara karanta wannan

Kaico: Ƴan bindiga sun hallaka basarake, sun yi awon gaba da mata da ƙananan yara

Malam Uba Sani.
'Yan bindiga sun yi garkuwa da malamin addinin Musulunci a Kaduna Hoto: Uba Sani
Asali: Twitter

Jaridar The Nation ta tattaro cewa maharan sun sace Sheikh Isma'il Gausi ne yayin da suka kutsa kai cikin gidansa ranar Laraba, 7 ga watan Augusta da daddare.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka sace Sheikh Gausi

Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa ƙarar harbe-harben ya jefa mutane cikin fargaba da tsoron abin da ka iya zuwa ya dawo, Punch ta ruwaito.

Mutumin wanda ya nemi a sakaya bayanansa ya kuma yi kira ga hukumomin tsaro da gwamnati su yi duk mai yiwuwa wajen ceto malamin cikin ƙoshin lafiya.

"Ƙarar harbe-harben da suka yi na da ban tsoro, mu na ganin lokacin da ‘yan bindigar suka tafi da Sheikh da karfi. Muna cikin damuwa matuka kan abin da ya faru.
"Muna kira ga hukumomin tsaro su yi iya bakin ƙokarinsu wajen ceto mana malamin mu da muke ƙauna," in ji majiyar.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai mummunan hari, sun kashe mutane sama da '30' a Arewa

Har kawo yanzu dai babu wata sanarwa a hukumance daga rundunar ƴan sanda ko gwamnatin jihar Kaduna kan sace Sheikh Isma'il Gausi.

Maharan sun kashe basarake a Kaduna

A wani rahoton kuma kun ji cewa ƴan bindiga sun kashe Magajin Gari da wani mutum ɗaya a lokacin da suka kai hari kauyen Gefe da ke ƙaramar hukumar Kajuru a Kaduna

Wani shugaban al'umma, Markus Ɗanja ya ce maharan sun buɗe wuta kan mai uwa da wabi, sannan sun tafi da mata da ƙananan yara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262