Zanga Zanga: Sifeta Janar Na ’Yan Sanda Ya Shiga Matsala Kan Kisan Matasa
- Sifeta-janar na 'yan sandan Najeriya ka iya rasa mukaminsa saboda zargin kashe-kashe yayin gudanar da zanga-zanga
- Kwamitin gudanarwa na masu zanga-zanga a jihar Lagos ya bukaci Bola Tinubu ya sallami Kayode Egbetokun daga mukaminsa
- Kwamitin ya zargi rundunar da sakaci tare da kisan mutane akalla 40 yayin zanga-zanga da ake yi a Najeriya kan halin kunci
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Kwamitin gudanar da zanga-zanga a Najeriya ya bukaci daukar mataki kan sifeta-janar na 'yan sandan kasar.
Kwamitin ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya sallami Kayode Egbetokun daga mukamin shugaban 'yan sandan kasar.
An bukaci sallamar sifeta-janar na 'yan sanda
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamitin ya fitar a Lagos a yau Juma'a 9 ga watan Agustan 2024, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matasan sun bukaci sallamar Egbetokun daga mukaminsa saboda zargin kashe-kashe da rundunar 'yan sanda ta yi yayin zanga-zanga, TheCable ta tattaro.
Ana zargin 'yan sanda da kisan matasa
Wannan na zuwa ne bayan masu zanga-zanga a Ojota da ke Lagos sun ayyana kwanaki uku a matsayin ranakun jimami ga wandanda suka rasa ransu.
Wani mamban kwamitin kuma mai magana da yawun kungiyar kare hakkin dan Adam, Hassan Taiwo ya tabbatar da haka.
Taiwo ya ce akalla mutane 40 ne suka rasa rayukansu ba bisa hakki ba yayin da ake gudanar da zanga-zanga.
"Muna bukatar a kori sifeta-janar na 'yan sanda a Najeriya saboda rasa rayuka da aka yi yayin zanga-zanga."
- Cewar kwamitin zanga-zanga
Sanusi II ya gargadi matasa kan zanga-zanga
Kun ji cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya shawarci matasa kan bari ana amfani da su domin lalata rayuwarsu ta gobe a kasar.
Sarkin ya nuna damuwa kan yadda matasa suka kai hari cibiyar NCC da ake shirin kaddamarwa a wannan mako da muke ciki.
Sanusi II ya tura sakon jaje ga al'umma da gwamnatin jihar Kano da Gwamnatin Tarayya da kuma ma'aikatar sadarwa a Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng