Kano: Abba Ya yi Goma ta Arziki ga Yan Banga, ya Karrama Wanda Ya Mutu a Bakin Aiki

Kano: Abba Ya yi Goma ta Arziki ga Yan Banga, ya Karrama Wanda Ya Mutu a Bakin Aiki

  • Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta yi goma ta arziki ga wasu yan banga bisa nuna bajintaru
  • Daraktan ayyuka na musamman a gidan gwamnatin Kano, AVM Ibrahim Umar mai ritaya ne ya jagoranci karrama yan bangar
  • Gwamnatin Kano ta raba kyautar kuɗi, kayan abinci da lambar karramawa ga yan bangar a yau Jumu'a 9 ga watan Agusta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Gwamnatin Kano ta karrama wani dan banga da aka kashe a bakin aiki a kwanakin baya.

Haka zalika gwamnatin ta karrama wani dan banga da ya samu munanan raunuka yayin da yake hana miyagu sata.

Kara karanta wannan

Tinubu zai fitar da N280bn: An shirya karasa gina kilomita 82 na babban titin Arewa

Yan banga
Gwamnatin Kano ta karrama yan banga. Hoto: Nabeel Sanusi Kofar Mazugal
Asali: Facebook

Legit ta tatttaro yadda bikin karramawar ya gudana ne a cikin wani bidiyo da Nabeel Sanusi Kofar Mazugal ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin jihar Kano ta karrama dan banga

Gwamnatin Kano ta karrama dan bangar da aka kashe yana sasanta mutane mai suna Bashir Auwal.

Bayan lambar yabo da ka ba shi, an ba iyalansa buhunan shinkafa biyu, N500,000 ga matarsa da kuma kudi N50,000 ga iyayensa guda biyu.

Gwamnatin Kano ta karawa dan banga matsayi

A daya bangaren, gwamnatin ta kara matsayi ga dan bangan da ya samu raunuka yana ƙoƙarin hana miyagu sata.

Dan bangar, Yunus Ibrahim Yunus da aka fi sani da Baba Kukawa ya samu kyautar N50,000 da buhun shinkafa bayan an kara masa matsayi.

Yan banga: Jawabin gwamnatin Kano

Daily Trust ta wallafa cewa AVM Ibrahim Umar mai ritaya ya ce sun yi kyautar ne domin kara karfafa gwiwar yan bangar wajen kara kokari a jihar.

Kara karanta wannan

Hauhawar farashi: Abba Gida Gida ya ji koken jama'a, gwamna ya sa labule da 'yan kasuwa

Ya kuma kara da cewa za su cigaba da ba su kulawa wajen tabbatar da walwalarsu domin inganta aikinsu a jihar.

Gwamnatin Kano za ta gina ofis

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Kano karkashin gwamna Abba Kabir Yusuf ta ware makudan kudi domin yin wasu ayyuka.

Daga cikin ayyukan da gwamnatin za ta yi, ta ambaci samar da ofis ofis ga masu taimakawa gwamna Abba Kabir Yusuf da ma'aikatar sufuri.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng