Kaduna: Motar Golf Ta Yi Taho Mu Gama da Gingimari, Ana Tsoron Dukkanin Fasinjoji Sun Mutu

Kaduna: Motar Golf Ta Yi Taho Mu Gama da Gingimari, Ana Tsoron Dukkanin Fasinjoji Sun Mutu

  • Jama'a sun shiga tashin hankali a yankin Gwargwaje, a karamar hukumar Zaria bayan motoci biyu sun yi karo da juna
  • Shugaban hukumar kare afkuwar hadurra a Kaduna, Kabir Nadabo ya bayyana cewa mutum 11 sun rasu nan take
  • FRSC ta bayyana cewa hadarin ya auku ne tsakanin wata babbar mota da karamar mota kirar Golf da ta sakin hannunta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna - An tafka gagarumar asarar rayuka a jihar Kaduna bayan motoci biyu sun yi taho mu gama da juna a Zaria.

Hadarin ya afku tsakanin babbar mota dauke da fasinjoji guda hudu da motar Golf dauke da mutane 11 a daidai Gwangwaje a karamar hukumar Zaria, Kaduna.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai mummunan hari, sun kashe mutane sama da '30' a Arewa

Accident
Mutane 11 sun rasu a hadarin mota Hoto: Gabrieletamborrelli
Asali: Getty Images

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa dukkanin fasinjojin motar ta Golf sun rasu nan take, yayin da sauran mutanen hudun cikin babbar motar su ka samu raunuka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Golf ta yi karo da babbar mota a Kaduna

Hukumar kiyaye afkuwar hadurra ta kasa (FRSC) ta tabbatar da afkuwar wani mummunan hadari da ya yi sanadiyyar rasuwar maza 11, The Nation ta wallafa.

Shugaban hukumar a Kaduna, Kabir Nadabo ya bayyana cewa akwai kasuwar bakin titi a Gwargwaje, wanda ta sa wasu direbobin ke bin hannun daya

An kai gawarwakin asibiti bayan hadarin mota

Shugaban FRSC a Kaduna, Kabir Nadabo ya ce mai motar Golf ya yi aron hannu kuma babu fitila a lokacin da aka yi karon da asubahin Juma'a, nan take duk fasinjojin motar su ka rasu.

Ya ce yanzu haka an mika gawarwakin zuwa asibitin koyar da Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria.

Kara karanta wannan

An samu sabanin tsakanin 'yan sanda da rundunar sojoji a kan harbin 'yan zanga zanga

Tirela da karamar mota sun yi karo

A wani labarin kun ji cewa rundunar 'yan sandan Jigawa ta tabbatar da afkuwar wani mummunan hadarin mota da ya yi sanadiyyar rasuwar mutane 14.

Hadarin ya afku bayan direban wata mota kirar Toyota ta nufi shingen da jami'an kula da shige da fice ke binciken wata babbar mota, a nan ne aka yi karo.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.