An Sake Tafka Babban Rashi, Tsohon Ɗan Majalisar Tarayya Ya Kwanta Dama

An Sake Tafka Babban Rashi, Tsohon Ɗan Majalisar Tarayya Ya Kwanta Dama

  • An sake yin babban rashi bayan mutuwar tsohon dan Majalisar Tarayya a yau Juma'a 9 ga watan Agustan 2024
  • Marigayin mai suna Wole Diya ya rasu yana da shekaru 63 a duniya bayan fama da jinya na wani lokaci
  • Diya, kafin rasuwarsa ya wakilci mazaɓar Somolu da ke jihar Lagos na wa'adi biyu bayan zama ɗan Majalisar jiha

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Lagos - An shiga jimami bayan mutuwar tsohon dan Majalisar Wakilai a jihar Lagos.

Marigayin Wole Diya ya rasu ne a yau Juma'a 9 ga watan Agustan 2024 da shekaru 63 a duniya.

Tsohon dan Majalisar Tarayya ya yi bankwana da duniya
Tsohon dan Majalisar Tarayya, Wole Diya ya kwanta dama a Lafia. Hoto: House of Representatives.
Asali: Facebook

Tsohon dan Majalisa ya rasu a Lagos

Kara karanta wannan

An samu baraka tsakanin shugaban Majalisar Tarayya da mataimakinsa? an gano gaskiya

The Nation ta tattaro cewa tsohon dan Majalisar ya rasa ransa kwanaki kadan kafin bikin zagayowar ranar haihuwarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Diya ya wakilci mazabar Somolu da ke jihar Lagos har na tsawon wa'adi biyu a Majalisar Tarayya, cewar Sahara Reporters.

Kafin zama ɗan Majalisar Tarayya, Diya ya wakilci mazabar Somolu a Majalisar jihar na tsawon wa'adi biyu.

Sakwannin ta'aziyya ga marigayin a Lagos

Shugaban karamar hukumar Bariga, Kolade David ya tabbatar da mutuwar marigayin inda ya ce an tafka babban rashi.

David ya ce marigayin mutum ne nagari wanda ya ba da gudunmawa sosai a cikin al'umma.

Har ila yau, shugaban karamar hukumar, Somolu, Hon. Abdul Hamed Salawu ya ce marigayin mutumin kirki ne da ya kamata a yi koyi da shi.

Marigayin kani ne ga marigayi Janar Oladipo Diya wanda ya rike mukamin tsohon hafsan sojojin Najeriya.

Kara karanta wannan

Ana ƙoƙarin shawo kan Ndume, dan majalisa ya kara tsige gaskiya ga Tinubu

Wanan na zuwa ne bayan rasa mambobin Majalisar Tarayya da dama a cikin ƴan kwanakin nan.

Fitacciyar mawakiya ta rasu a Najeriya

Kun ji cewa fitaciyyar marubuciya kuma mai rera waka kuma ‘yar wasan kwaikwayo, Ms Onyeka Onwenu ta rasu.

An rahoto cewa jarumar ta Nollywood, Ms Onwenu ta rasu da yammacin ranar Talata a Asibitin Reddington da ke Legas jim kadan bayan rera waka.

Onwenu ta yi wasa ne a wajen bikin ranar haihuwar Misis Okoli, likitan hada magunguna, kuma wacce ta kafa kamfanin sarrafa magunguna na Emzor.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.