Tinubu Ya yi Ruwan Manyan Muƙamai a Jihar Arewa, Gwamna ya Mika Saƙon Godiya

Tinubu Ya yi Ruwan Manyan Muƙamai a Jihar Arewa, Gwamna ya Mika Saƙon Godiya

  • Gwamnatin jihar Katsina ta mika sakon godiya ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan ba yan asalin jihar muƙamai a gwamantin tarayya
  • Mukaddashin gwamnan jihar Katsina, Faruk Lawal Jobe ne ya miƙa sakon godiya ga shugaban kasar Najeriya a madadin gwamnatin jihar
  • Cikin waɗanda shugaba Bola Tinubu ya ba muƙamai a gwamantinsa akwai tsohon gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari da sauransu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - Gwamantin Jihar Katsina ta mika godiya ga shugaban kasa Bola Tinubu bisa karrama ƴaƴanta da muƙamai.

Mukaddashin gwamnan jihar, Malam Faruk Lawal Jobe ne ya yi godiya ga shugaban kasar a madadin gwamantin jihar.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP a Arewa ya shiga matsala kan sukar Tinubu, an gindaya masa sharuda

Faruk Lawal Jobe
Gwamnatin Katsina ta yi godiya ga Tinubu kan raba mukamai. Hoto: Ibrahim Kaulaha Muhammad
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa cikin wadanda aka ba manyan muƙamai akwai tsohon gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wadanda aka ba muƙamai a Katsina

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da nada Aminu Bello Masari ya jagoranci majalisar gudanarwar hukumar TETFUND.

Haka zalika Tinubu ya nada Kabir Mashi a matsayin kwamishinan tarayya a ma'ikatar tattara haraji ta RMAFC, sai kuma Abdullahi Imam da aka ba manaja a ma'aikatar raba kudi ta kasa.

Gwamnan Katsina ya yi godiya ga Tinubu

Mukaddashin gwamnan jihar Katsina, Faruk Lawal Jobe ya mika godiya ga shugaban kasa a madadin gwamnatin jihar.

Leadership ta wallafa cewa Malam Faruk Jobe ya ce sun gode wa shugaban kasa bisa amincewa da kwarewar mutanen Katsina har ya ba su jagoranci.

Sakon gwamna ga wadanda aka ba mukami

Kara karanta wannan

Shugaban APC ya fadawa Tinubu hanyar da zai shirya da talakawa bayan zanga zanga

Malam Faruk Lawal Jobe ya taya waɗanda suka samu muƙamin murna inda ya ce suna da kwarewa a fannoni daban daban.

Ya kuma kara da cewa suna da karfin gwiwa kan za su yi amfani da kwarewarsu wajen kawo sauyi a Najeriya.

Tinubu ya nada manyan mukamai

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya yi ruwan mukamai a hukumomi daban-daban na gwamnatin tarayya.

Bola Ahmed Tinubu ya nada dan tsohon gwamnan jihar Kwara, Cornelius Oluwasegun Adebayo a matsayin shugaban NALDA.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng