ICPC Ta Dura Ma’ikatar Aikin Hajji Kan Zargin Karkatar da N90bn, Ta Kama Daraktan NAHCON

ICPC Ta Dura Ma’ikatar Aikin Hajji Kan Zargin Karkatar da N90bn, Ta Kama Daraktan NAHCON

  • Hukuma mai yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ICPC ta dira ofishin hukumar alhazai ta kasa kan zargin cin hanci da rashawa
  • ICPC ta kai samame hedikwatar hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) ne bisa zargin salwantar da kudi N90bn a aikin Hajjin shekarar 2024
  • Hukumar ICPC ta bayyana dalilin da yasa ta kai samame ofishin NAHCON duk da cewa akwai damar gayyatar jami'ai domin tattaunawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Hukumar ICPC ta kai samame hedikwatar hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) a birnin tarayya Abuja.

ICPC ta bayyana babban dalilin da yasa ta kai samamen tare da wasu jami'an hukumar NAHCON da ta kama.

Kara karanta wannan

Kaduna: Motar golf ta yi taho mu gama da gingimari, ana tsoron dukkanin fasinjoji sun mutu

ICPC Najeriya
ICPC ta kai samame NAHON kan zargin karkatar da kudi. Hoto: ICPC Nigeria.
Asali: Facebook

Jaridar the Guardian ta wallafa cewa ICPC ta dakatar da wasu ayyuka a hedkwatar yayin samamen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

ICPC ta kai samame hedikwatar NAHCON

Hukumar ICPC ta kai samame hedikwatar NAHCON domin zargin karkatar da kudin tallafin aikin Hajji N90bn.

A yayin samamen, ICPC ta dakatar da ayyuka a muhimman ofisoshin ma'aikatar da suka hada da ofishin harkar tattara kudi.

Hukumar ICPC ta kama daraktan NAHCON

Bayan rashin gamsuwa da bayanan da ta samu, ICPC ta tafi da wani darakta a hedikwatar NAHCON domin zurfafa bincike.

Jami'in yada labaran hukumar, ICPC Demola Bakare ya tabbatar da kai samamen ya kuma ce hakan na cikin wasu bincike da suke a hedikwatar NAHCON.

Dalilin kai samame hedikwatar NAHCON

Legit ta ruwaito cewa Demola Bakare ya bayyana cewa kai samamen ya zama musu dole ne kasancewar sun mika gayyata ga wasu jami'an NAHCON amma sun yi biris da su.

Kara karanta wannan

NNPC ke yiwa tattalin arziki zagon kasa? Kyari ya wanke kamfanin Najeriya

Amma duk da haka, Demola Bakare ya bayyana cewa suna binciken ne a bisa kan doka oda ba tare da cin mutunci ba.

Gwamnan Neja ya koka kan aikin NAHCON

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago ya nuna takaicinsa kan yadda hukumar NAHCON ta tafiyar da ayyukan Hajjin bana.

Gwamna Bago ya yi kira ga majalisar tarayya da ta binciki tallafin N90bn da gwamnatin tarayya ta bayar domin gudanar da aikin Hajjin bana.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng