Shugaban APC Ya Fadawa Tinubu Hanyar da Zai Shirya da Talakawa Bayan Zanga Zanga

Shugaban APC Ya Fadawa Tinubu Hanyar da Zai Shirya da Talakawa Bayan Zanga Zanga

  • Shugaban jam'iyyar APC a kasar Amurka, Farfesa Tai Bolafin ya ba shugaban kasa Bola Tinubu shawara kan gamsar da talakawan Najeriya
  • Tai Bolafin ya kuma fadi manyan matsalolin da gwamnatin shugaba Bola Tinubu ke fuskanta da ya kamata a magance su cikin gaggawa
  • Haka zalika shugaban jam'iyyar ya yi kira ga yan Najeriya kan cigaba da hakuri da nuna goyon baya ga gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Yayin da ake cigaba da kokawa kan gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, shugaban APC a kasar Amurka ya yi magana.

Shugaban APC a kasar Amurka, Farfesa Tai Bolafin ya ba Tinubu muhimmiyar shawarar wajen gamsar da talakawa kan ayyukansa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya ƙara daukan matakin ragewa talaka raɗaɗin cire tallafin man fetur

Shugaba Tinubu
Shugaban APC ya ba Bola Tinubu shawara. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta bayyana cewa Farfesa Tai Bolafin ya yi maganar ne yayin da ya kai ziyara birnin tarayya Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shawarar shugaban APC ga Bola Tinubu

Farfesa Tai Bolafin ya yi kira ga gwamnatin Tinubu kan bayyana ayyukan cigaba da yayi a kowane lokaci domin fahimtar da talakawa.

Tai Bolafin ta ce kuskure ne sai an shiga wata damuwa sannan a fito da ayyukan wanda hakan ba lallai ya gamsar da talakawa ba.

Ya kuma kara da cewa manyan ayyuka da Tinubu ya yi ba a yada su ga yan kasa yadda ya kamata ba saboda haka ga bukaci a canza salon isar da sako ga al'umma.

APC: Manyan matsalolin mulkin Tinubu

Farfesa Bolafin ya bayyana cewa manyan matsalolin da suke jefa Najeriya a wahala sun hada da rashin yan kasa na gari da cin hanci da rashawa.

Kara karanta wannan

Tsohon Shugaban CDD ya ragargaji Tinubu, Farfesa ya fadi abin da ya fusata talaka

Jaridar Blueprint ta wallafa cewa Farfesan ya ambaci wasu tsare tsaren da shugaban kasa ya kawo a matsayin dalilan shiga wahala a Najeriya.

Sai dai duk da haka ya bukaci yan Najeriya su kara hakuri da cigaba da goyon bayan Bola Tinubu domin sauki na zuwa a gaba.

Shugaba Tinubu zai kawo motocin CNG

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta kara motsawa domin ganin ta magance radadin cire tallafin fetur da ya jefa talakawa cikin wahalar rayuwa.

A makon nan ne aka ji cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gana ga shugaban kamfanin motocin Innoson domin samar da motocin CNG a Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng