Zanga Zanga: Matashi a Kano Ya Yi Barazanar Kashe Kakakin Rundunar 'Yan Sanda
- Rundunar 'yan sandan Kano ta yi aiki tukuru wajen kama masu tayar da hatsaniya a lokacin zanga-zanga
- Daga bisani jami'in hulda da jama'a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana cafke sama da mutane 632 da ake zargi da sata
- Da alama kamen ya yiwa wasu matasa zafi, inda wani Isma'il Yusif ya yi ikirarin kashe SP Abdullahi Kiyawa
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Nasarorin da rundunar 'yan sandan Kano ke bayyanawa, musamman ta fuskar cafke barayin lokacin zanga-zanga ya jawo barazana.
Wani fusataccen matashi, Ismail Yusif ya yiwa jami'in hulda da jama'a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa zagin tsamen nama a shafin Facebook.
PRNigeria ta tattaro Ismail Yusif ya yi wa SP Kiyawa ruwan ashariya, inda ya zarge shi da rashin son cigaban yaran talakawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matashi ya yi ikirarin kashe kakakin 'yan sanda
Matashi Ibrahim Yusif ya cire kunya, ya yi wa jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa barazana.
Matashin ya ce da zai hadu da SP Kiyawa, sai ya kawo karshen rayuwarsa saboda ba ya kaunar ci gabansu bayan kama barayin zanga-zanga.
Barazanar kashe kakakin 'yan sandan Kano
Legit ta tuntubi SP Abdullahi Haruna Kiyawa ta shafin sada zumunta, inda ya tabbatar da cewa matashin da ma wasu sun dade su na zagin jami'an tsaro.
Mun tattaro cewa shi kan shi matashin da ke amfani da sunan Isma il M Yusif, a Facebook ya dade ya na yi wa jami'an yan sandan zagin kare dangi.
Sai dai SP Kiyawa wanda ya aiko mana da wasu bidiyon zagin jami'an, ciki har da Sufeton yan sanda Kayode Egbetokun, bai yi magana a kan daukar mataki ba.
Zanga-zanga: Kotu ta yi hukunci
A baya kun ji cewa kotun tafi da gidanka da ma'aikatar shari'a ta samar a ofishin rundunar 'yan sandan Kano ta yi hukunci a kan masu zanga-zanga da ake zargi da tarzoma.
Kotun ta yi umarnin aika matasa 632 da aka damke zuwa gidan kaso har zuwa ranar 19 Agusta 2024 da za a dawo kotun domin ci gaba da sauraron shari'ar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng