Shari’ar Zaben Gwamna: Rikici Ya Barke Tsakanin Masoyan APC da SDP a Wata Jihar Arewa
- An fara musayar baki tsakanin jam'iyyar APC mai mulki da jam'iyyar adawa ta SDP a jihar Kogi kan shari'ar zaben gwamna
- A yayin da SDP ke zargin APC da fara bikin murnar yin nasara a kotun Koli, ita kuma APC ta ce jam'iyyar adawa ke yada labaran karya
- Masoyan jam'iyyun siyasar biyu na zargin juna da 'murnar wuri' tun gabanin Kotun Koli ta fara zama kan shari'ar zaben jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kogi - Rikici ya barke tsakanin magoya bayan APC mai mulki a jihar Kogi da na jam'iyyar adawa ta SDP gabanin hukuncin Kotun Koli kan zaben gwamnan jihar.
An ce siyasar Kogi ta kara daukar zafi yayin da magoya bayan jam'iyyun biyu suka fara gudanar da murnar samun nasara tun kafin kotun ta fara zama kan shari'ar.
Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa majalisar yakin zaben SDP ta zargi gwamnatin Kogi da yin bikin murnar nasarar da ta ce ta samu a shari’ar gwamnan da ake yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
SDP ta zargi APC da 'yin murnar wuri'
A wata sanarwa da Isaiah Ijele Davies, kakakin kwamitin yakin neman zaben SDP ya fitar, jam’iyyar ta ce bikin murnar da jami'an gwamnati da masoyan APC ke yi 'bai dace ba.'
SDP ta yi zargin cewa a ranar Talata, 6 ga watan Agusta, magoya bayan APC sun yi ta yada jita-jita a shafukan sada zumunta cewa su ne suka samu nasara a shari’ar.
A cewar sanarwar:
“Wannan bikin murnar wanda ya hada da yada hotunan taya Ahmed Usman Ododo na APC murna, ya faru ne duk da cewa har yanzu kotun koli ba ta fara zamanta kan shari'ar zaben ba."
APC ta zargi SDP da 'yada jita-jita'
A martanin da daraktan yada labarai na kwamitin yakin zaben PDP, Kingsley Femi Fanwo ya mayar, ya zargi SDP da yada labaran karya a duk lokacin da kotu ta yanke wani hukunci.
Ya kuma soki jam’iyyar SDP da yin farfaganda da tunzura jama’a, inda ya ce APC ta yi amanna da bin doka da oda yayin da abokan hamayyarsu ke yada jita-jita, inji jaridar Daily Trust.
"Jam'iyyarmu ba ta da sha'awar shiga cikin harkar karairayi, yada farfaganda, tunzura jama'a, da bikin murna na karya."
- Inji martanin Fanwo.
SDP Vs APC: Kotu ta fadi gwamnan Kogi
A wani labarin, mun ruwaito cewa kotun sauraron kararrakin zaben gwamna ta ayyana Ahmed Usman Ododo na APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Kogi.
Kotun ta yi fatali da ƙarar da jam'iyyar SDP da dan takarar gwamnanta, Murtala Ajaka suka shigar bisa dalilin sun gaza tabbatar da zargin da suke yi kan waɗanda ake ƙara.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng