Ya Gama Sukar Tinubu, Matsala 1 Ta Taso Gwamnan PDP Ya Nemi Agajin Shugaban Kasa

Ya Gama Sukar Tinubu, Matsala 1 Ta Taso Gwamnan PDP Ya Nemi Agajin Shugaban Kasa

  • Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya ziyarci babbar hanyar da ta hada Kano zuwa Maiduguri inda ruwan sama ya cinye hanyar a Katagum
  • An ruwaito cewa ruwa kamar da bakin kwarya ne ya lalata hanyar a dai dai kauyukan Malori-Guskuri, lamarin da ya katse zirga-zirgar jama'a
  • Gwamnan ya roki gwamnatin Bola Tinubu da ta kawo dauki domin a gyara hanyar wadda ta hada Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Bauchi - Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya roki gwamnatin tarayya da ta kawo dauki domin gyara titin Kano zuwa Maiduguri da ruwa ya cinye shi a dai dai Katagum.

Kiran na zuwa ne kwanaki bayan gwamnan Bauchi ya caccaki Shugaba Bola Tinubu inda ya ce tsare-tsaren gwamnatin tarayyar ba su da tasiri ga 'yan kasa.

Kara karanta wannan

PDP ta shirya daukar Tinubu aiki a zaben 2027, gwamna ya fadi kuskuren gwamnatin APC

Gwamnan PDP ya roki taimakon gwamnatin tarayya domin gyara titin Kano - Maiduguri
Gwamnan Bauchi ya roki gwamnatin tarayya ta gaggauta gyara titin Kano Maiduguri. Hoto: @SenBalaMohammed, @officialABAT
Asali: Twitter

Ruwa ya ci titin Kano zuwa Maiduguri

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ruwan sama kamar da bakin kwarya ya yi mummunar barna a babbar hanyar gwamnatin tarayya da ta hada Kano zuwa Maiduguri.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce ruwan saman ya ci babbar hanyar musamman a kauyukan Malori-Guskuri da ke karamar hukumar Katagum a jihar Bauchi.

Barnar da ruwan ya yi ta katse hanyar, lamarin da ya sa ababen hawa ba za su iya bi ta kan hanyar ba sai dai su nemi wata hanyar ta daban.

Gwamnan PDP ya nemi taimakon Tinubu

Gwamnan Bauchi, Bala Muhammad ya ziyarci yankin da lamarin ya shafa domin duba halin da ake babbar hanyar take ciki, inji rahoton Tribune.

Gwamnan wanda ya ci zabe a PDP ya jaddada muhimmancin wannan hanya da ta hada yankin Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: abin da Ministan Tinubu ya fadawa Sanusi II da miyagu suka lalata cibiyar NCC

Ya roki gwamnatin tarayya da ta kawo dauki cikin gaggawa domin gyara hanyar da ta lalace, yana mai jaddada muhimmancin saukaka zirga-zirgar kayayyaki domin amfanin ‘yan kasa.

Gwamnan Bauchi ya soki jawabin Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya caccaki jawabin da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi game da zanga-zangar yunwa da ake yi.

Gwamnan ya ce ya kamata gwamnatin tarayya ta daina ba ‘yan Najeriya uzuri game da halin da ake ciki, yana mai cewa tsare-tsaren Tinubu ne suka jefa 'yan kasar a cikin wahala.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.