PDP Ta Gamu da Matsala: Kotu Ta Hana Jam’iyyar Adawa Gudanar da Taro a Arewa

PDP Ta Gamu da Matsala: Kotu Ta Hana Jam’iyyar Adawa Gudanar da Taro a Arewa

  • Wata babbar kotun jih a Benuwai ta hana PDP gudanar da babban taron da ta shirya yi a ranar Asabar, 10 ga watan Agusta, 2024
  • Kotun ta ce PDP ba za ta iya gudanar da taron zaben shugabannin gundumomi ba har sai an yanke hukuncin kan karar da ke gabanta
  • A karshen Yuli ne PDP ta yi taron gundumomin, sai dai an zargi wasu shugabannin jam'iyyar da sace kayan zabe a kanan hukumomi shida

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Benuwai - Wata babbar kotu mai zamanta a karamar hukumar Gboko a jihar Benuwai ta dakatar da PDP daga gudanar da taron gundumomi a kananan hukumomi shida.

Kara karanta wannan

DSS ta warware rudanin da aka shiga bayan an kai samame ofishin NLC saboda zanga zanga

An ce kotun ta dakatar da PDP daga gudanar da taro a Buruku, Gboko, Guma, Kwande, Ushongo, and Konshisha da ta shirya yi a ranar 10 ga Agustan 2024.

Kotu ta yi hukunci kan taron kananan hukumomi na jam'iyyar PDP a Benuwai
Benuwai: Kotu ta dakatar da PDP daga gudanar da taron kananan hukumomi. Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

Benuwai: Kotu ta dakatar da taron PDP

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kotun ta ce dakatarwar za ta ci gaba da aiki har sai an kammala bincike kan hargitsa taron da aka yi a ranar 27 ga Yulin, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun da fari, Sanata Emmanuel Orker Jev da wasu 'yan jam'iyyar ne suka shigar da kara wadda ta sa kotun ta yanke wannan hukunci domin kare muradun wadanda abin ya shafa.

Kotun ta ce ba za a gudanar da taron jam'iyyar a kananan hukumomin da abin ya shafa ba har sai an yanke hukunci kan shari'ar yayin da za a saurari karar 16 ga Agusta.

Kara karanta wannan

Ogun: Hukumar zabe ta sanar da ranar zaben ciyamomi, an kafawa jam'iyyu sharudda

Rikici ya barke a PDP bayan taro

Sai dai an ce wannan hukuncin kotun ba zai zama cikas ga babban taron jam'iyyar na jiha da za a gudanar a ranar 31 ga Agusta ba, inji rahoton The Punch

Idan za a iya tunawa, a ranar 27 ga Yuli, 2024 ne PDP ta yi taronta na gundumomi, sai dai an zargi wasu shugabannin jam'iyyar da sace kayan zabe a kanan hukumomin da abin ya shafa.

Wannan rikici da ya tashi daga zabukan gundumomin ya kai ga raba jam'iyyar zuwa gida biyu, inda har aka dakatar da wasu shugabannin jam'iyyar daga kowanne tsagi.

PDP ta dakatar da tsohon gwamna

A wani labarin, mun ruwaito cewa PDP ta dakatar da tsohon gwamnan jihar Benuwa, Samuel Ortom bisa zarginsa da aikata zagon kasa ga jam'iyyar.

An dakatar da Ortom ne har na tsawon wata daya tare da wasu mutane guda uku da ake zarginsu da hana ruwa gudu a tarurrukan da jam'iyyar ta sha shiryawa a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.