Dan Majalisa Ya Cire Tsoro Ya Fadi Babbar Asarar da Najeriya Ta Yi Saboda Buhari
- Wani ɗan majalisar wakilai daga jihar Osun ya fito ya caccaki shekara takwas da Muhammadu Buhari ya kwashe yana mulki
- Honarabul Omirin Emmanuel Olusanya ya bayyana cewa shekara takwas da Buhari ya yi yana mulki babbar asara ce ga Najeriya
- Ɗan majalisar ya nuna cewa saboda girman ɓarnar da Buhari ya bari, duk wanda ya hau kan mulkin Najeriya sai an yi ƙorafi
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Legas - Ɗan majalisar wakilai daga jihar Osun, Honorabul Omirin Emmanuel Olusanya, ya caccaki mulkin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
Omirin Emmanuel ya bayyana cewa wa'adi biyu na mulkin Shugaba Buhari babbar asara ce ga ƙasar nan.
Ɗan majalisa ya caccaki Muhammadu Buhari
Ɗan majalisar ya bayyana hakan ne a yayin da ake bude taron Bojah World a Legas, lokacin da yake zantawa da manema labarai, cewar rahoton jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa shekara takwas da Shugaba Buhari ya yi yana mulki a ƙasar nan, sun zama asara ga Najeriya, rahoton Daily Post ya tabbatar.
"Ɓarnar da ya bari, ko Yesu Almasihu ne ya zama shugaban ƙasan Najeriya, musamman a irin wannan lokacin, mutane sai sun ci gaba da yin ƙorafi."
"Domin kusan irin halin ɓarnar da ake ciki, har yanzu ba mu fara aiki da kasafin kuɗin shekarar 2024 ba."
"Kamata ya yi a ce zuwa wata mai kamawa, mun fara shirya kasafin kuɗin shekarar 2025."
"Ni mamba ne a kwamitin kuɗi na majalisar wakilai. Saboda haka na san abin da yake faruwa a halin yanzu."
- Honarabul Omirin Emmanuel Olusanya
Karanta wasu labaran kan Buhari
- Tinubu ya fatattaki wanda Buhari ya naɗa mukami, ya maye gurbinsa da Dantsoho
- Masu zanga zanga sun dira gidan Buhari a Daura, bayanai sun fito daga Katsina
- An gano abin da ya faru da masu zanga-zanga suka nufi gidan Buhari da Sarkin Daura
'Dan siyasa ya faɗi illolin Buhari ga Arewa
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar APC na ƙasa a yankin Arewa maso yamma, Lukman Salihu ya bayyana kurakuran da Muhammadu Buhari ya yi a baya.
Lukman Salihu ya ce Buhari bai amfani Arewa da komai ba sai jawo mata tarin matsaloli da yayi a tsawon lokacin da ya kwashe kan karagar mulki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng