Uju Kennedy: Mamaki Ya Kama Jama'a bayan Ministar Harkokin Mata Ta Tarwatsa Taro
- An shiga mamaki bayan an gano ministar mata da kanta ta tarwatsa wani taro da ke gudana a babban birnin tarayya Abuja
- Minista Uju Kennedy Ohanenye ta bayyana cewa ana gudanar da taron da sunan ma'aikatarta wacce ba ta san zancen ba
- Ministar wacce ta isa taron a fusace ta ce shugaban kasa bai ji dadin yadda ake gudanar da taron da sunan gwamnatin tarayya ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Hankali ya karkarta birnin tarayyar kasar nan bayan an hango Ministar mata, Uju Kennedy Ohanenye ta fasa wani taro.
Da take jawabi a fusace, Ministar ta bayyana cewa ana gudanar da taron da sunan ma'aikatarta bayan babu abin da ya hada su da shi.
Ministar matan Najeriya ta tashi taro
A bidiyon da ta wallafa a shafinta na Facebook, Misis Uju Kennedy ta bayyana cewa sai da aka sanar da masu shirya taron cewa ba za su shiga cikin shirin ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta ce an sanar da Mela-Chiyoma PAT Limited da ke shirya taron cewa shugaban kasa bai amince su shige shi ba, amma ta yi biris da umarnin.
'Yan sanda sun kama mai shirya taron
Jaridar Leadership ta wallafa cewa jami'an tsaro sun cafke wacce ta shirya wani taro da har yanzu ba a san na menene ba a Abuja.
Hakan ya biyo bayan tarwatsa taron da Ministar ma'aikatar mata, Uju Kennedy Ohanenye ta yi a ranar Alhamis.
Ministar ta bayyana cewa wanda ta shirya taron na hannun jami'an DSS, kuma za a dauki matakin ladabtarwa a kanta, tare da jan kunnen masu shirin yi wa ma'aikatarta sojan gona.
'Yan sanda sun damke kasugurmin barawo
A wani labarin kun ji cewa rundunar 'yan sandan Kano ta damke wani kasungurmin barawo da ya dade ya na addabar jama'a da sace-sace.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da kamen da jami'ansu su ka yi, inda aka gano bindigu da tarin harsashi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng