“Abin da Ya Hana Mu Cikawa Talakawa Alkawarin da Muka Yi Musu”: ’Yan Majalisa
- Majalisar Wakilai ta ba 'yan Najeriya hakuri kan rashin cika alkawarin da ta yi na tallafawa da rabin albashin mambobinta
- Majalisar ta ce ta himmatu wurin tabbatar da cika alkawarin inda ta ce kawai an samu jinkiri ne saboda wasu ka'idoji
- Wannan na zuwa ne bayan Majalisar ta yi alkawarin rage albashin mambobinta da kaso 50 domin tallafawa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Majalisar Wakilai ta yi magana kan dalilin kin cika alkawarin ba da rabin albashin mambobinta ga talakawa.
Majalisar ta kuma fayyace gaskiya kan cewa suna daukar albashin N900,000 wanda ta ce kwata-kwata ba gaskiya ba ne.
Alkawarin Majalisa ga talakawa a halin kunci
Mai magana da yawun Majalisar, Akin Rotimi shi ya yi wannan martanin a jiya Laraba 7 ga watan Agustan 2024 a shafin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce Majalisar ta himmatu wurin tabbatar cika alkawarin da ta dauka a ranar 18 ga watan Yulin 2024.
Majalisar ta dauki alkawarin rage albashin mambobinta da kaso 50 domin tallafawa al'umma har na tsawon watanni shida.
"Muna bakin cikin rashin cika alkawarin da muka yi a watan Yulin 2024 saboda wasu matsaloli."
"Mun dauki alkawarin ne wanda kowane mamba zai ba da gudunmawa a zaman Majalisar sai dai ba a tabbatar da hakan a hukumance ba sai ranar 23 ga watan Yuli."
- Akin Rotimi
Musabbin rashin cikawa talakawa alkawari
Rotimi ya ce an samu taskago ne saboda wasu ka'idoji da dole za a bi da suka shafi harkokin kudi.
Ya ce an riga an wuce wurin kan tabbatar da hakan domin cika alkawarin da suka yi ga talakawa.
'Yan Majalisa sun rage albashi saboda talakawa
Mun kawo muku labarin cewa Majalisar Wakilai a Najeriya ta zaftare albashin mambobinta domin tallafawa al'umma yayin da ake shan fama.
Mambobin Majalisar sun amince da rage 50% na albashinsu saboda tallafawa al'umma yayin da ake cikin halin ƙunci.
Mataimakin kakakin Majalisar, Benjamin Kalu shi ya gabatar da bukatar a gaban Majalisar a ranar Alhamis 18 ga watan Yulin 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng