An Shiga Jimami Bayan Jirgi Dauke da Fasinjoji Ya Kone, An Rasa Rayukan Mutum 20

An Shiga Jimami Bayan Jirgi Dauke da Fasinjoji Ya Kone, An Rasa Rayukan Mutum 20

  • Wani jirgin ruwa ɗauke da kayayyaki da fasinjoji ya gamu da hatsari a jihar Bayelsa wanda ya jawo asarar rayuka
  • Jirgin ruwan wanda ke kan hanyar zuwa birnin Yenagoa, babban birnin jihar ya gamu hatsarin ne bayan injinsa ya fashe ana cikin tafiya
  • Kakakin rundunar ƴan sandan jihar wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ya ce an rasa rayukan mutum 20 sakamakon hatsarin jirgin

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Bayelsa - Wani jirgin ruwa na katako mai suna ‘Godbless Dickson’ ɗauke da kaya da fasinjoji sama 64 da matuƙansa ya gamu da hatsari a jihar Bayelsa.

Jirgin ruwan da ya yi hatsarin ya kama da wuta ne wanda hakan ya jawo asarar rayukan mutum 20 da ke cikinsa.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Gwamnan Plateau ya dauki matakin saukakawa jama'a

Jirgin ruwa ya yi hatsari a Bayelsa
Mutum 20 sun rasu a hatsarin jirgin ruwa a Bayelsa Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Me ƴan sanda suka ce kan hatsarin?

Mummunan lamarin ya auku ne a ranar Laraba a kusa da ƙauyen Ezetu 1 da ke ƙaramar hukumar Southern Ijaw ta jihar Bayelsa, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Bayelsa, ASP Musa Mohammed, ya ce kawo yanzu mutane 20 ne aka tabbatar da mutuwarsu, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

Ya ƙara da cewa har yanzu jami'an tsaro na ci gaba da ƙoƙarin ceto sauran mutanen.

Jirgin ruwan wanda ke maƙare da kayayyakin amfanin gona daga ƙauyukan yankin yana kan hanyarsa ne ta zuwa kasuwar Swali a birnin Yenagoa, babban birnin jihar.

Yadda jirgin ruwan ya gamu da hatsari

Shugaban ƙungiyar ma’aikatan ruwa ta Najeriya reshen jihar Bayelsa, Mista Ogonipa Ipigansi, ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Matasa sun fusata da kisan ɗan uwansu, sun bankawa fadar basarake wuta a Arewa

"Jirgin ya bar ƙauyen Ezetu 1 da misalin ƙarfe 3:00 na rana. Yayin da suka kusa zuwa Okubie, injin da suke amfani da shi sai ya kama wuta da ya fashe. Hakan ya sa jirgin ya ƙone tare da nutsewa. Wasu daga cikin mutanen da ke cikin jirgin sun nutse."

- Mista Ogonipa Ipigansi

Ya bayyana cewa ƙungiyar ta aika da jiragen ruwa masu gudu zuwa wurin domin taimakawa fasinjojin da ke jirgin.

Ya bayyana cewa har yanzu ba a san adadin yawan mutanen da suka rasu ba saboda ana ci gaba da aikin ceto sannan fasinjoji da dama ba a gansu ba.

Jirgin sojoji ya yi hatsari

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jirgin sojin saman Najeriya ya tafka hatsari a ƙauyen Tani dake ƙaramar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.

Wani ganau ba jiyau ba, wanda ya buƙaci a ɓoye sunansa, ya ce lamarin ya faru ne wurin ƙarfe 5:00 na asuba, wanda ya haifar da tashin hankali ga mazauna yankin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng