Tsohon Shugaban CDD Ya Ragargaji Tinubu, Farfesa Ya Fadi Abin da Ya Fusata Talaka

Tsohon Shugaban CDD Ya Ragargaji Tinubu, Farfesa Ya Fadi Abin da Ya Fusata Talaka

  • Tsohon shugaban cibiyar cigaban dimokuraɗiyyar ta CDD ya yi managa kam halin kuncin rayuwa da talakawa a Najeriya suke ciki
  • Farfesa Jibril Ibrahim ya bayyana cewa kuskuren gwamantin shugaba Bola Tinubu ne ya jefa al'ummar Najeriya cikin mummunan hali
  • Jibril Ibrahim ya yi magana ne biyo bayan zanga zangar adawa da tsadar rayuwa da aka yi a Najeriya a kusan dukkan jihohin kasar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon shugaban CDD, Farfesa Jibril Ibrahim ya yi magana kan halin da ake ciki a Najeriya.

Farfesa Jibril ya zargi gwamnatin tarayya da rashin tsari wanda a cewarsa hakan ne ya jefa al'umma a wahalar rayuwa.

Kara karanta wannan

Ana ƙoƙarin shawo kan Ndume, dan majalisa ya kara tsige gaskiya ga Tinubu

Bola Tinubu
An bayyana alkawarin da Tinubu ya gaza cikawa. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Farfesa Jibril Ibrahim ya zargi gwamnatin shugaba Bola Tinubu da rashin cika alkawari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu: Abin da ya fusata yan Najeriya

Farfesa Jibril Ibrahim ya bayyana cewa salon mulkin Bola Tinubu ne ya fusata yan Najeriya, wanda hakan ne ya kai ga yin zanga zanga.

Ya kuma bayyana cewa samun tashin farashin kayayyaki ya jefa yan kasa da dama halin kwana da yunwa a fadin Najeriya.

Sai yaushe za a ga canji a Najeriya?

Daily Post ta wallafa cewa Farfesa Jibril Ibrahim ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta yi alkawari ga yan Najeriya kan samun sauƙin rayuwa amma sun gagara gani a kasa.

Ya ce kuncin rayuwa ya karu har inda ya kai mutane ba su da kudin sayen magani idan ba su da lafiya wanda hakan yasa hakurinsu ya kare.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: A karshe, Ganduje ya yi magana, ya tura sako ga 'yan Najeriya

Jibril: 'Tinubu ya gaza cika alkawari'

Farfesa Jibril Ibrahim ya bayyana cewa bayan cire tallafin mai gwamnatin Tinubu ta yi alkawarin kawo motocin CNG cikin sati uku da za su biyo baya.

Sai dai ya ce yanzu an doshi wata wata 13 ba tare da ganin alamar motocin ba, ga shi rayuwa ta yi tsada ga talaka.

Dattawan Kudu sun soki Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar Delta Obedient Elders' Council ta yi zazzafan martani ga Bola Ahmed Tinubu kan maganar da ya yi a kan masu zanga zanga.

Kungiyar ta ce maganar da shugaban kasa ya yi tana nuna cewa tamkar bai san halin kuncin da talakawa ke ciki a Najeriya ba ne.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng