Bidiyon Rashawa: Jami’in Shige da Fice ya Tsunduma a Matsala, An Dakatar da Shi

Bidiyon Rashawa: Jami’in Shige da Fice ya Tsunduma a Matsala, An Dakatar da Shi

  • Hukumar shige da fice ta kasa ta dauki mataki mai tsauri kan jami'inta mai suna Okpravero Ufuoma kan bidiyonsa da ya yadu a kafafen sada zumunta
  • Masu amfani da kafafen sada zumunta sun yada bidiyonsa yayin da aka nuna shi yana shirin karbar kudi a wajen matafiya a filin jirgin sama
  • Rahotanni sun nuna cewa Shugaban hukumar shige da fice, Kemi Nandap ce ta bayyana dalilin daukan matakin a yau Alhamis, 8 ga watan Agusta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Hukumar shige da fice ta kasa ta dauki mataki mai tsauri a kan wani jami'inta da ake zargi da karɓar na goro.

Kara karanta wannan

DSS ta warware rudanin da aka shiga bayan an kai samame ofishin NLC saboda zanga zanga

Jami'in mai suna Okpravero Ufuoma ya bazu a duniya ne a cikin wani bidiyo da aka yada a kafafen sada zumunta.

Kemi Nandap
Hukumar shige da fice ta dakatar da jami'inta. Hoto: @nigimmigration
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa shugabar hukumar shige da fice ta kasa Kemi Nandap ce ta sanar da lamarin a yau Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da ake zargin Okpravero da aikatawa

Masu amfani da kafafen sada zumunta sun yada wani bidiyon da ake nuna Okpravero Ufuoma yana neman karbar kudi.

A bisa bidiyon ne ake zargin jami'in da karbar cin hanci a hannun matafiya a wani filin jirgin saman Najeriya.

Hukumar shige ta fice ta yi martani

Shugabar hukumar shige da ficen Najeriya, Kemi Nandap ta ce abin da jami'in ya aikata ba yana nuna haka suke aiki ba kwata kwata.

Haka zalika Kemi Nandap ta ce abin takaici ne yadda jami'in ya so zubar da tarbiyyar girmama baki da hukumar ta ba su.

Kara karanta wannan

Jami'an DSS sun kai samame hedkwatar NLC bayan gano wani sirri kan zanga zanga

An dakatar da jami'in hukumar shige ta fice

Business Day ta wallafa cewa Kemi Nandap ta bayyana cewa an dakatar da jami'in daga aiki har sai an kammala bincike a kansa.

Ta kuma bayyana cewa matakin da suka dauka na cikin kokarin da gwamnatin Bola Tinubu take na kawo sauyi a Najeriya.

Abia: An dakatar da jiga jigan APC

A wani rahoton, kun ji cewa ga dukkan alamu rigima na neman ɓarkewa a jam'iyyar APC reshen jihar Abia a lokacin da aka dakatar da wasu manyan jiga-jigai.

Masu ruwa da tsakin APC a Aba ta Arewa sun yanke shawarar dakatar da wasu bisa zargin rashin ɗa'a, ladabi da kuma sojan gona.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng