Ribar Zanga Zanga: An Fara Maganar Yunkurin Inganta Rayuwa a Arewa

Ribar Zanga Zanga: An Fara Maganar Yunkurin Inganta Rayuwa a Arewa

  • Sanata mai wakiltar Neja ta Gabas ya yi kira na musamman ga shugabannin Arewa bayan gama zanga zangar adawa da tsadar rayuwa
  • Muhammad Sani Musa ya bayyana matakan da ya kamata a dauka domin ganin an samu sauyin rayuwa a Arewacin Najeriya
  • Legit ta tattaauna da shugaban dalibai a jami'ar jihar Gombe domin jin irin rawar da dalibai za su taka a irin wannar tafiyar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Sanata Muhammad Sani Musa daga jihar Neja ya yi kira kan kawo gyara a Arewacin Najeriya.

Sanatan ya bukaci shugabannin Arewa su zauna domin kawo sauyin da zai kawo cigaba a yankin.

Kara karanta wannan

Ned Nwoko: Fitaccen sanatan PDP ya mutu a kasar Switzerland? Gaskiya ta fito

Majalisa
An yi kira ga shugabannin Arewa kan kawo sauyi. Hoto: Nigerian Senate
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Sanata Muhammad Sani Musa ya ambaci abubuwan da ya kamata a mayar da hankali a kai a Arewa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin neman inganta rayuwa a Arewa

Sanata Muhammad Sani Musa ya ce yadda yan Arewa suka rika daga tutar Rasha da kwadayin mulkin soja ya nuna akwai babbar damuwa.

Sanatan ya kara da cewa yin sace sace da wasu matsaloli da aka samu sun nuna akwai kalubale babba a gaban al'ummar Arewa.

Kira ga shugabannin Arewa

Sanatan ya ce ya kamata tun daga kan mataimakin shugaban kasa, shugaban majalisar wakilai su zauna domin samo mafita.

Ya kara da cewa taron ya kamata ya haɗa da dukkan gwamnonin jihohi, ministoci, yan majalisar tarayya da na jihohi da dukkan masu ruwa da tsaki.

Sauyin da za a kawowa mutanen Arewa

Within Nigeria ta wallafa cewa Sanata Muhammad Sani Musa ya ce ya kamata shugabannin su kawo sauyi a harkar noma, kiwo, ilimi da tsaro a yankin Arewa.

Kara karanta wannan

Gwamna ya fadi babban darasin da gwamnonin Arewa suka dauka daga zanga zangar yunwa

Ya kuma tabbatar da cewa wannan kokarin ya zama wajibi su fara shi saboda Allah zai tambayesu a kan shugabancin da suke yi.

Legit ta tattauna da Mustapha Abubakar

Wani shugaban dalibai a jami'ar jihar Gombe, Mustapha Abubakar ya zantawa Legit cewa maganar da sanatan ya fada tana kan hanya.

Mustapha Abubakar ya ce dalibai za su bayar da gudunmawa sosai wajen kawo sauyi idan aka sanya su a cikin tafiyar.

Arewa: Matasa sun yi kira ga Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyoyin Arewa sun buƙaci Bola Tinubu da gwamnonin jihohin Arewa su tashi tsaye wajen warware damuwar al'umma.

Shugaban gamayyar kungiyoyin na Zamfara, ya yi kira ga shugaban ƙasa ya sake nazari kan matakin da ya ɗauka kamarsu cire tallafi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng