Gwamna Ya Fadi Darasin da Ya Kamata Gwamnonin Arewa Su Dauka Kan Zanga Zanga
- Gwamnan jihar Bauchi ya bayyana darasin da ya kamata gwamnonin Arewa su ɗauka sakamakon zanga-zangar da ake yi a faɗin ƙasar nan
- Gwamna Bala Mohammed ya bayyana cewa ya kamata gwamnonin su farka domin yin abin da ya dace a yankin
- Ya kuma caccaki jawabin da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kan zanga-zangar, inda ya ce shugaban ƙasa bai faɗi wani abu mai amfani ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya yi magana kan zanga-zangar yunwa da ake yi a faɗin ƙasar nan.
Gwamna Bala ya bayyana cewa zanga-zangar hannunka mai sanda ce a gare shi da sauran gwamnonin Arewacin Najeriya kan su tashi wajen samar da shugabanci mai kyau a yankin.
Me Gwamna Bala ya ce kan zanga-zanga?
Gwamna Bala ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Bauchi a lokacin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen jam'iyyar PDP na zaɓen ƙananan hukumomin jihar, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Za mu iya ganin cewa zanga-zangar ta ɗauki salo daban-daban. A Arewacin Najeriya, kira ne a gare mu domin mu farka mu kawo shugabanci na gari sannan mu mutunta jama'a."
"Akwai fushi da yunwa, ya kamata mu shawo kan matsalolinmu da suka hana mu samun ci gaba."
- Gwamna Bala Mohammed
Gwamna Bala ya caccaki jawabin Tinubu
Gwamna Bala Mohammed wanda shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin jam'iyyar PDP ya caccaki jawabin da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi kan zanga-zanga, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.
Gwamnan ya bayyana cewa babu wani abu mai amfani a cikin jawabin inda ya yi zargin cewa jawabin ya ƙara sanyawa zanga-zangar ta ƙara zafi.
Ya bayyana cewa kamata ya yi a ce Tinubu ya saurari gwamnoni ya ji abin da za su ce kafin ya fito ya yi wannan jawabin, saboda su ma suna sauraron abin da shugabannin ƙananan hukumomi ke cewa.
Gwamna Bala ya yiwa Tinubu shaguɓe
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya sake caccakar Bola Tinubu kan yadda ake gudanar da mulki.
Sanata Bala Mohammed ya ce zai gayyaci Bola Tinubu ya zama daraktan kamfe na jam'iyyar PDP a zaɓen 2027 da ake tunkara saboda ƴan Najeriya ba za su sake mayar da shi kan kujera ba.
Asali: Legit.ng