NLC Ta Yi Martani Mai Zafi Bayan Jami'an Tsaro Sun Kai Samame a Hedkwatarta
- Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta fito ta yi martani kan samamen da jami'an tsaro suka kai a hedkwatarta da ke birnin tarayya Abuja
- Jami'an tsaron waɗanda suka haɗa da ƴan sanda da DSS sun kai samame a hedkwatar NLC inda suka tafi da wasu takardu
- NLC ta yi Allah wadai da samamen wanda ta bayyana a matsayin abin kunya domin ko a lokacin mulkin soja ba a taɓa yi mata hakan ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta yi Allah wadai da samamen da jami'an tsaro suka kai a ofishinta da ke Abuja.
Jami'an tsaro da suka haɗa da ƴan sanda da jami'an hukumar DSS sun kai samame a hedkwatar NLC da ke Abuja bisa zargin cewa mambobin ƙungiyar sun ɗauki nauyin zanga-zangar #EndBadGovernance.
Wane martani NLC ta yi?
Da yake martani cikin wata sanarwa a shafin yanar gizo na NLC, kakakin ƙungiyar na ƙasa, Benson Upah, ya yi Allah wadai kan abin da jami'an tsaron suka yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Da misalin ƙarfe 8:30 na dare bayan an daɗe da tashi daga aiki, gungun jami'an tsaro ɗauke da makamai sun kai samame a hedkwatar ƙungiyar NLC da ke Abuja."
"NLC ta yi Allah wadai da wannan zubar da girman da jami'an tsaron Najeriya suka yi. Jami'an tsaron ba su nuna wata takarda ta doka ba wacce ta ba su iznin shiga harabar NLC a cikin tsakar dare."
"Ko a lokacin mulkin soja, jami'an tsaro ba su taɓa kai kai samame a ofishin ƙungiyar ƙwadago ba. Tabbas wannan abin baƙin ciki ne ga dimokuraɗiyyar Najeriya."
- Benson Upah
NLC ta zargi jami'an tsaro
Ƙungiyar NLC ta kuma umarci ma'aikatanta da su dakata da zuwa ofishin har sai an tabbatar da cewa jami'an tsaron ba su ajiye wani abu ba wanda zai iya jawo musu sharri.
Ta kuma buƙaci jami'an tsaron da su dawo da dukkanin takardun da suka ɗauke saboda ba su da hurumin ɗaukarsu daga ofishin.
NLC ta ba Tinubu shawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta ba Shugaba Bola Tinubu shawarar yadda zai dakile shirin gudanar da zanga-zanga.
Kungiyar NLC ta ce hanya daya mafi dacewa wurin dakile zanga-zangar ita ce tattaunawa da fusatattun matasan da ke son fitowa kan tituna domin nuna adawarsu da gwamnati.
Asali: Legit.ng