Bayan Zanga Zanga, Mai Neman Takaran Shugaban Kasa a APC Ya Caccaki Gwamnati

Bayan Zanga Zanga, Mai Neman Takaran Shugaban Kasa a APC Ya Caccaki Gwamnati

  • Malamin addini kuma ɗan siyasa, Tunde Bakare ya yi zazzafan martani ga gwamnatin tarayya kan zanga zangar kuncin rayuwa
  • Fasto Tunde Bakare ya caccaki gwamnatin tarayya kan maganar cewa ana daukan nauyin zanga zangar adawa da tsadar rayuwa
  • Haka zalika malamin ya fadi abin da ya kamata gwamnati ta yi idan tana so talakawa su yarda da maganar ba su hakuri da take yawan yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Malamin addini kuma tsohon mai neman takarar shugaban kasa a APC ya yi martani ga gwamnatin Bola Tinubu.

Fasto Tunde Bakare ya ce akwai buƙatar gwamnatoci su canza salon da suke mulkan talakawa a Najeriya.

Kara karanta wannan

Minista ya tona asirin gwamnoni, ya faɗi gwamna da ke sauya shinkafar tallafin Tinubu

Tunde Bakare
Fasto Tunde Bakare ya yi kira ga gwamnatin Najeriya. Hoto: Pius Utomi Ekpei
Asali: Getty Images

Jaridar Punch ta wallafa cewa Tunde Bakare ya ce ya kamata musu mulki su rika aikata abin da suke fadawa talakawa a kan hakuri da wahalar rayuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An dauki nauyin zanga zanga a Najeriya?

Fasto Tunde Bakare ya ce maganar da gwamnatin tarayya ta yi na cewa ana daukar nauyin zanga zanga ba gaskiya ba ce.

Malamin ya ce yunwa da wahalar rayuwa ne suka matsawa talakawa zuwa zanga zangar ba wani abu ba.

Tunde Bakare ya kuma nuna muhimmancin zama a tattauna domin shawo kan matsalolin Najeriya maimakon tayar da hankulan al'umma.

Bakare ya yi kira ga yan siyasar Najeriya

Fasto Tunde Bakare ya yi kira na musamman ga yan siyasa kan nuna dattaku a kan wahalar rayuwa da ake ciki.

Ya ce talakawa ba za su yarda su gansu suna cin dukiyar ƙasa ba sannan kuma suna ba su hakuri kan wahalar rayuwa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta sake magana kan dawo da tallafin man fetur da kawo saukin abinci

Tunde Bakare ya ce sam bai kamata shugabanni suna ci su koshi, su yi ƙiba sannan su bar talakawa cikin wahala ba.

Zanga zanga: Al-Mustapha ya yi magana

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon mai tsaron Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha ya yi bayani kan mulkin soja da wasu ke ribibi a yau.

Manjo Hamza Al-Mustapha mai ritaya ya yi tsokaci kan masu daga tutar kasar Rasha yayin zanga zangar tsadar rayuwa a wasu jihohin Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng